"Karya ne," Gwamnati ta Yi Magana Kan Amincewa da Biyan Albashin Akalla N105, 000
- Awanni ƙalilan bayan labarin mafi karancin albashi ya bayyana a Najeriya, gwamnatin tarayya ta musanta labarin da ta bayyana da cewa babu kamshin gaskiya cikinsa
- Dazu ne wasu rahotanni suka ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi sabon lissafin mafi karancin albashi daga ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun
- A ranar Talata kungiyar kwadago ta janye yajin aikin sai baba ta gani da ta fara a ranar Litinin domin tabbatar da gwamnati ta dubi bukatunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Awanni kadan bayan bullar rahoton sabon mafi karancin albashi, gwamantin tarayya ta musanta hakan.
Dazu ne rahotanni suka ce ministan kuɗi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ya mika saboda lissafin N105,000 a matsayin mafi karancin albashi ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Daily Trust ta tattaro cewa kwamitin da gwamnati ta kafa kan mafi karancin albashi ya cimma matsaya da kungiyoyin kwadago.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani kwamitin ya shaidawa shugaba Tinubu matsayar da aka cimma, inda shi kuma ya umarci ministan ya buga lissafi.
Nawa ne ainihin mafi karancin albashin?
Tun bayan janye yajin aiki da kungiyoyin kwadago suka shiga a ranar Litinin ne suka shiga tattaunawa da kwamitin gwamnati kan mafi karancin albashin.
Rahotanni dai na cewa an samu maslaha tsakanin kungiyoyin da ke neman a biya N494,000 da gwamnati mai ikirarin N60,000 kawai za ta iya biya.
Zancen N105, 000 ba gaskiya ba ne
Zuwa yanzu ba a fito a hukumance ko daga kungiyar NLC ko gwamnati an yiwa jama'ar Najeriya bayani ba, amma hadimin shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Wale Onanuga ya musanta cewa N105,000 ne sabon albashin.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, hadimin shugaban kasar ya ce labarin shugaba Tinubu ya karbi tayin kudin ba gaskiya ba ne.
Wannan na nufin har yanzu ba a san nawa ne kungiyoyin kwadago suka amince gwamnati za ta iya biyan ma'aikata ba.
Gwamnati ta musanta dawo da tallafin fetur
A baya kun ji cewa gwamnatin tarayya ta musanta cewa an dawo tallafin man fetur kuma ana biyan kudin a boye.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi gwamnati ta fadawa 'yan Najeriya gaskiya kan batun cire tallafin man fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng