Gwamnatin Najeriya Ta Yi Albishir Kan Aikin Jirgin Kasan Legas Zuwa Kano

Gwamnatin Najeriya Ta Yi Albishir Kan Aikin Jirgin Kasan Legas Zuwa Kano

  • Ana sa ran ƙaddamar da jirgin kasan da zai fara hada-hada daga Legas zuwa Kano a yau Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024
  • Ministan sufuri, Sa'idu Ahmed Alkali ne ya bayyana haka tare da karin haske kan yadda jigilar jirgin kasan za ta kasance
  • A kwanakin baya ne ma'aikatar sufuri ta kasa ta sanar da cigaba da gyaran layin dogon Kano zuwa Legas domin fara zirga zirga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Ministan sufuri, Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya bayyana cewa jirgin kasan Kano zuwa Legas zai fara zirga zirga a yau Alhamis.

Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya bayyana cewa titin jirgin zai dawo aiki ne bayan an masa wasu gyare-gyare.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

Jirgin kasa
Jirgin kasan Kano zuwa Legas zai fara aiki. Hoto: Sa'idu Ahmed Alkali
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Alkali ya ce dawo da titin jirgin aiki na cikin kokarin Bola Tinubu na cigaba da ayyukan da ya gada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amfanin jirgin kasan Lagos-Kano

Ministan sufuri ya tabbatar da cewa za a samu alfanu sosai saboda dawowar aikin da jirgin kasan zai yi a yau musamman a harkar tattalin arziki.

Ya ce za a samu sauƙin hada-hadar kaya tsakanin Kudu da Arewa musamman ma a yanzu da farashin man fetur ya tashi.

Sanata Alkali ya kara da cewa za a kara samun raguwar haduran da ake a kan titunan Najeriya wanda suke jawo asarar rayuka da dukiya.

A karkashin haka, ya ce ana sa ran samun sauƙin farashin kayan masarufi a kasuwannin Najeriya saboda sauƙin da jirgin kasan zai samar.

Kara karanta wannan

Hukumomin Saudiyya sun gargadi maniyyata a shirin hajjin bana

Kokarin Tinubu a aikin jirgin kasan

Sanata Alkali ya ce karasa gyaran tashar jirgin na daga cikin manyan abubuwan da shugaba Bola Tinubu ya dauka domin inganta sufuri a Najeriya.

Ya kuma kara da cewa idan gwamnatoci masu zuwa za su yi tunanin samar da wasu jiragen kasan da sauran ayyukan cigaba to za a yi nasarar ciyar da Najeriya gaba.

Kungiyar NLC ta janye yajin aiki

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suke yi a fadin kasar na tsawon mako guda.

Rahotanni sun nuna cewa hakan ya biyo bayan wani taro na musamman da majalisar zartarwar kungiyoyin ta kasa da suka yi a safiyar Talata a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng