Zargin El Rufai Ya Saci N423bn: Lauya Ya Ba Gwamnatin Kaduna Muhimmiyar Shawara
- An yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta ba Nasir El-Rufai damar kare kansa kan tuhume-tuhumen almundahana da ake yi masa
- Wani lauya mai kare hakkin ɗan Adam, Mike Ozekhome ne ya yi wannan kiran yana mai gargadin gwamnatin kan yin aikin da-na-sani
- Wannan na zuwa ne bayan da kwamitin majalisar ya zargi tsohon gwamnan jihar da karkatar da Naira biliyan 423 da cin zarafin ofis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Wani lauya mai kare hakkin ɗan Adam, Mike Ozekhome ya nemi a ba Nasir El-Rufai damar kare kansa kan zargin ya yi almundahana a lokacin ya na gwamnan Kaduna.
Kwamitin da majalisar Kaduna ta kafa domin bincikar gwamnatin El-Rufai ce ta nemi a tuhumi tsohon gwamnan, tare da gurfanar da shi kan zargin cin zarafin ofis da almundahana.
Lauya Ozekhome, a zantawarsa da Channels TV ya ce a yayin da kwamitin ya gama aikinsa, to ya kamata shi ma El-Rufai a ba shi damar da zai kare kansa daga tuhume-tuhumen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A bar El-Rufai ya kare kansa" - Lauya
A cewar lauyan:
"Ni ba Allahn musuru ba ne da zan ce na san abin da zai faru gobe, amma dai ina ga akwai bukatar a ba El-Rufai damar kare kansa.
"A yayin da majalisar ta mika rahoton ga gwamnan jihar, wasu za su ce ai N423bn ba kananan kudi ba ne, kawai a gurfanar da tsohon gwamnan, wanda yin hakan kai tsaye kuskure ne."
Lauya Ozekhome ya ce El-Rufai na da ikon da zai iya zuwa kotu ya yi ƙarar majalisar jihar kan wadannan tuhume-tuhume da suke yi masa, "doka ta ba shi wannan damar".
"Kar ayi gaggawar tuhumar El-Rufai" - Lauya
Lauyan ya kuma gargadi majalisar Kaduna da ma gwamnatin jihar da ta guji yin gaggawar gurfanar da tsohon gwamnan kan abin da ba su tabbatar ba.
Ozekhome ya ce:
"Shin majalisar jihar ta gayyace shi domin amsa tambayoyi? An ba shi damar kare kansa ne amma bai amsa gayyata ba? Saboda akwai abubuwan dubawa kafin zartar da hukunci.
"Kai tsaye ba za ka dora wa mutum laifi a kan abin da ba ka tabbatar ba, musamman a irin wannan lamari da ya shafi ta'addanci. Kuskure ne daukar irin wannan matakin na gaggawa."
Ana zargin El-Rufai ya karkatar da N423bn
Tun da fari, mun ruwaito cewa kwamitin da majalisar Kaduna ta kafa domin ya binciki tsohuwar gwamnatin jihar ya zargi Nasir El-Rufai da cin zafin ofis da kuma almundahana.
A yayin da kwamitin ya nemi a tuhumi El-Rufai kan karkatar da N423bn, ya kuma ba da shawarar a tuhumi kwamishinonin da suka yi aiki tare da tsohon gwamnan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng