“Dalili 1 da Ya Sa NLC e Zuzuta Albashin Ƴan Majalisun Tarayya”, Inji Hon. Rotimi

“Dalili 1 da Ya Sa NLC e Zuzuta Albashin Ƴan Majalisun Tarayya”, Inji Hon. Rotimi

  • Majalisar wakilai ta zargi 'yan kwadago da yayata labarin karya game da albashin 'yan majalisun tarayya da nufin harzuka jama'a
  • Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya ce labaran karya da NLC ke yadawa yana zama cin mutunci ga majalisar
  • A hannu daya kuma, majalisar ta goyi bayan inganta albashin ma'aikata amma ta zargi 'yan kwadago da yiwa tattalin arziki zagon kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya ce kungiyoyin kwadago suna yada "labarai marasa tushe" game da albashin 'yan majalisar dokokin kasar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akin Rotimi ya kuma caccaki 'yan kwadagon kan rufe muhimman ma'aikatu yayin yajin aikin da suka yi a fadin kasar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

Majalisar wakilai ta yi magana kan yajin aikin 'yan kwadago
Majalisar wakilai ta zargi 'yan kwadago da yada jita-jita kan albashin 'yan majalisu. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Mai magana da yawun majalisar ya ce majalisar wakilai na "goyon baya" ga kiran da ake yi na inganta albashi da yanayin aiki ga ma'aikata a cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yi hattara da karin albashi" - Majalisa

Ya gargadi cewa:

"Akwai bukatar yin taka-tsan-tsan wajen kara mafi karancin albashi. Idan ya zarce karfin tattalin arzikinmu to zai jawo hauhawar farashin kayayyaki, korar ma'aikata daga aiki, da sauran illolin tattalin arziki."
"Don haka, akwai bukatar mu tunkari wannan batu ta hanya madaidaiciya domin tabbatar da ma'aikata, gwamnati da tattalin arziki ba su takura ba na dogon lokaci."

Majalisa ta ce akwai kuskure a yajin-aaikin NLC

Jaridar Vanguard ta ruwaito sanarwar mai magana da yawun majalisar wakilan ta ci gaba da cewa:

“Hakazalika, alkiblar yajin aikin da 'yan kwadagon suka shiga kafin dakatar da shi ya jefa mu a damuwa, saboda akwai babban kalubalen da ka iya haifarwa a gaba.

Kara karanta wannan

Kungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki, ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako 1

“Rufe muhimman ma'aikatu, kamar tashar wutar lantarki ta kasa, ya zama zagon kasa ga tattalin arziki kuma yana da illa ga rayuwar kasarmu da jama'ar ta."

NLC na zuzuta albashin 'yan majalisu

Hon. Akin Rotimi ya ce yana da muhimmanci a magance jita-jitar da shugabannin ƙwadago ke yadawa game da albashin 'yan majalisu.

“'Yan kwadago sun kwashe shekaru suna yada labaran karya game da albashin ‘yan majalisun tarayya, duk domin su harzuka jama’a da kuma zubar da mutuncin majalisar.
“Wadannan karairayin na karkatar da hankalin jama'a daga muhimman batutuwan da ke faruwa da kuma cin mutuncin majalisar, wanda ya kamata 'yan kwadago su daina."

- Akin Rotimi.

'Yan kwadago sun janye yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun janye yajin aikin da suka shiga a ranar Litinin bayan ganawarsu da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja.

A yayin ganawar, shugabannin kwadago da wakilan gwamnatin sun cimma matsaya kan abin da ya shafi mafi karancin albashin ma'aikatan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.