An Samu Sabani a Majalisa Tsakanin Sanatoci Kan Dokar Hana Makiyaya Yawo

An Samu Sabani a Majalisa Tsakanin Sanatoci Kan Dokar Hana Makiyaya Yawo

  • Majalisar dattijai ta yi karatu na biyu ga kudurin hana makiyaya yawon kiwo a fadin Najeriya a jiya Laraba, 5 ga watan Yuni
  • Sanatan jam'iyyar APC daga jihar Benue, Titus Tartenger Zam ne ya gabatar da kudurin ga majalisar ganin yadda ake rikici da makiyaya
  • Sai dai kudirin ya samu suka wajen sanatoci daga yankin Arewa da kungiyar Miyetti Allah mai kare hakkin makiyaya a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Majilisar dattijai ta yi karatu na biyu ga kudurin da zai hana makiyaya yawo a faɗin Najeriya a jiya Laraba.

'Dan majalisar dattijai daga jihar Benue, Titus Tartenger Zam ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

Majalisar dattijai
Majalisa na yukurin hana makiyaya yawo a Najeriya. Hoto: The Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Titus Tartenger Zam ya bayyana cewa kudurin zai kawo sauki ga makiyaya da ma sauran al'umma baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da kudirin makiyaya ya ƙunsa

An yi ikirarin an kawo kudurin ne domin rage sabani tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya da samar da zaman lafiya.

Idan aka zartar da kudurin, za a yiwa makiyaya matsuguni a jihohin su ba tare da barin su suna yawo gari gari da sunan kiwo ba, rahoton the Cable.

"A bar makiyaya su yi yawo" - Sanatoci

Sai dai sanatoci daga jihohin Arewa sun soki kudurin ganin cewa hakan zai zama an take hakkin makiyayan ne.

Sanatocin da suka soki kudurin sun hada da Danjuma Goje, Adamu Aliero, Sulaiman Kawu Sumaila, Hussein Babangida Uba da Barau Jibrin.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana bayan an zarge ta da kisan fararen hula

Kungiyar Miyetti Allah ta kare makiyaya

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da kudurin tana mai cewa hakan ya saɓa da kundin mulkin kasa.

Shugaban Miyetti Allah, Adamu Toro ya ce idan za a tilasta makiyaya su dawo garuruwan su na asali to dole a tilasta sauran 'yan kasa ma su koma garuruwan su.

Manoma da makiyaya sun yi sulhu

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar manoma da makiyaya sun saka hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Kudancin Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa dokar wacce ta shafi yankin kudu maso yammacin Najeriya an tabbatar da ita ne a Ibadan hedikwatar jihar Oyo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel