Mafi Karancin Albashi: Dalilin Gaza Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnati da 'Yan Kwadago

Mafi Karancin Albashi: Dalilin Gaza Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnati da 'Yan Kwadago

  • Tattaunawar da aka yi a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, tsakanin wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayya ba ta haifar da wani ƙwaƙƙwaran sakamako ba
  • 'Yan kwamitin yanke sabon mafi ƙarancin albashin sun dai tattauna ne domin samo mafita kan albashin da za a riƙa biyan ma'aikata
  • An ɗage taron domin ba ministan kuɗi, Wale Edun, lokaci ya cika wa’adin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba shi na gabatar masa da lissafi kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An tashi ba tare da cimma matsaya ba a tattaunawar wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi.

Hakan ya faru ne bayan gwamnatin tarayya ta gaza yin sabon tayi kan abin da za ta riƙa biya a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

NLC: Muhimman abubuwan da aka tattake wuri a kansu a taron mafi ƙarancin albashi

An kasa cimma matsaya tsakanin gwamnati da 'yan kwadago
Za a sake zama tsakanin 'yan kwadago da wakilan gwamnati kan mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce tawagar gwamnatin tarayya ta kasa gabatar da sabon tayin da ya wuce N60,000 da tayi a makon jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taron tattaunawar da aka koma wanda aka fara da misalin ƙarfe 3:30 na rana a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, ba a samu cimma matsaya ba.

Mafi ƙarancin albashi: An ɗage tattaunawa

Hakan ya biyo bayan gazawar gwamnatin Shugaba Tinubu na gabatar da sabon tayi kan abin da za ta riƙa biyan ma'aikata.

"An ɗage taron ne domin a ba ministan kuɗi lokaci ya cika wa’adin da shugaban ƙasa ya ba shi ya gabatar masa da lissafin abubuwan da za a kashe."
"Mun yi shawarwari gaba ɗaya sannan su (tawagar gwamnatin tarayya) suka ce suna buƙatar a dage zaman saboda suna buƙatar su kai bayanan ga shugaban ƙasa."

Kara karanta wannan

"Yadda Tiinubu yake biyan tallafin fetur bayan sanar da soke tsarin tun ranar farko"

"Kun san Shugaba Bola Tinubu ya ba su wa’adi domin su ba shi bayani kan abin da ya kamata."
"Domin haka za mu iya fahimtar cewa ba su da wani abin da za su ba mu tun da ba su ba shugaban ƙasa bayanin lissafin abin da za a kashe ba."

- Wata majiya

Kwamitin wanda ya ƙunshi wakilan gwamnatin tarayya da na jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin kwadago zai ci gaba da tattaunawa a ranar Alhamis 6 ga watan Yuni da ƙarfe 2:00 na rana.

Albashin da ya kamata ta biya ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa na kusa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, Daniel Bwala, ya bayyana mafi ƙarancin albashin da ya kamata gwamnati ta biya ma'aikata.

Daniel Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya ya kasance N250,000 duba da yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel