Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Fadar Sarki Inda Suka Yi Awon Gaba da Matarsa
- Ƴan bindiga sun kai hari fadan sarki a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da matarsa a cikin duhun dare
- Maharan sun farmaki fadar Sarkin Ninzo a karamar hukumar Sanga da ke jihar a daren jiya Laraba 5 ga watan Yuni
- Rundunar ƴan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta watau ASP Mansir Hassan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - An shiga wani irin yanayi a daren jiya Laraba 5 ga watan Yuni bayan harin ƴan bindiga a jihar Kaduna.
Maharan sun kutsa fadar basarake a Ninzo, Alhaji Umar Musa da ke karamar hukumar Sanga.
Kaduna: Ƴan bindiga sun sace matar sarki
Ƴan bindigan sun kai harin ne tare da sace mai dakin basaraken inda aka baza jami'an ƴan sanda domin ceto matar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar ƴan sanda a Kaduna, ASP Mansir Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin.
Mansir ya tabbatar da cewa rundunar ya baza jami'anta cikin dazukan Sanga domin ceto matar da aka sace, The Guardian ta tattaro.
Kungiya ta bukaci tura sako ga al'umma
Kungiyar ci gaban yankin Ninzo ta yi Allah wadai da kokarin kai harin wanda ya yi sanadin bacewar matar sarkin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Moses Audi da sakatarenta, Silas Anche suka sanyawa hannu.
Kungiyar ta bukaci al'umma da su zauna lafiya da kai zuciya nesa tare da ba gwamnati hadin kai domin shawo kan lamarin.
Kaduna: Masu kwacen waya sun hallaka soja
A wani labarin, kun ji cewa wasu ‘yan daba da suka kware wajen satar waya da sauran laifuka sun kashe wani jami’in soja, Laftanar I.M Abubakar.
Rahotanni sun tabbatar cewa masu kwacen wayar sun kashe sojan ne a Unguwan Sarki da ke cikin birnin Kaduna a cikin makon nan.
Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da kisan sojan inda ya bukaci hukumomi su dauki matakai kawo karshen matsalar da ake dama da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng