Gwamnatin Gombe Ta Kawo Salon Canza Fasalin Almajiranci a Arewa

Gwamnatin Gombe Ta Kawo Salon Canza Fasalin Almajiranci a Arewa

  • Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da canza salon yadda tsarin almajiranci ke tafiya wajen shigo da tsare-tsaren zamani
  • Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkar tsangaya da almajiranci, Aminatu Sheikh Dahiru Usman Bauchi ce ta fadi haka
  • Legit ta tattauna da wani mai karantarwa a makarantar allo, Abubakar Salihu domin jin yadda suka kalli shirin da gwamnatin ke yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta amsa kiran da aka daɗe ana yi kan kawo gyara a harkar almajiranci a Najeriya.

Gwamnatin da dauki matakin samar da adadin almajirai a fadin jihar kan kokarin saka tsare-tsaren zamani a harkar almajiranci.

Kara karanta wannan

Bayan fasa gidajen gyaran hali kusan 20 a Najeriya, an fadawa Tinubu dabarar da zai dauka

Gwamna Inuwa Yahaya
Za a kawo gyara a harkar almajiranci a Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai ba gwamnan jihar shawara kan almajiranci da karatun tsangaya, Aminatu Sheikh Dahiru Bauchi ce ta bayyana sababbin tsare-tsaren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za ayi rijistar almajirai a Gombe

Sayyada Aminatu Dahiru Bauchi ta bayyana cewa gwamnatin Gombe za ta yi rijistar dukkan makarantun tsangaya da almajirai da ke fadin jihar.

Ta ce an dauki matakin ne domin sanin adadin almajirai da suke Gombe da kuma garuruwan da suka fito domin samun sauki idan aka fara kawo gyara a harkar.

Za a shigar da almajirai cikin NIMC

Har ila yau, Sayyada ta kara da cewa za ta yi haɗaka da hukumar rijistar 'yan kasa (NIMC) wajen shigar da almajirai tsarin.

Idan aka samu nasarar hakan, ta ce za a ba dukkan almajirai katin shaida domin kare su daga tsangoma a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

Almajiranci: Sayyada tayi kira ga iyaye

Sayyada Aminatu ta ce abin Allah wadai ne yadda iyaye ke watsi ya yaran su da sunan sun tura su makarantu a birane.

Ta kara da cewa yanzu zamani ya canza saboda haka dole iyaye su dauki mataki kan karatun ƴaƴansu maimakon kai su almajiranci ba tare da wata kulawa ba.

Legit ta tattauna da Abubakar Salihu

A hirar da Legit ta yi da wani malami a makarantar allo, Abubakar Salisu ya bayyana cewa matukar gwamnati ga gaske take tsarin zai yi kyau.

Ya ce hakan zai taimaka wajen wayar da kan almajirai kan ilimin zamani da rage tsangoma da waresu gefe da ake a cikin al'umma.

An gyara wutar Arewa maso gabas

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar TCN ta sanar da kammala gyaran wutar lantarki a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Yankin ya yi fama da rashin wuta na tsawon sama da kwana 50 sakamakon lalacewar wasu layukan wuta da aka samu a tsakanin Gombe da Jos.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel