Mu na alfahari da almajiranci, bai kamata a hana ba - Adamu Garba

Mu na alfahari da almajiranci, bai kamata a hana ba - Adamu Garba

Tsohon Sanata daga jihar Yobe, Adamu Garba ya yi sharhi a kan jawabin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi a kan neman a soke almajiranci inda ya ce almajirancin abin alfahari ne ga Arewa.

A cewar Garba, almajirancin yana daga cikin al'addun arewa kuma babu wata hikima idan aka hana almajirancin, sai dai kawai ayi gyara cikin tsarin almajirancin.

Garba ya rubuta a Twitter cewa:

Almajiranci abin tunkaho ne da alfahari a wurin mu. Eh, mun yadda ayi gyara cikin a harkar amma ba wai a hana baki daya ba. Babu wata al'umma mai hankali da za ta yi watsi da al'addunta sai dai ta yi gyra. Dukkan kasashen da suka cigaba suka girmama abinda suka gada daga iyaye da kakanni, mene ya sa ba za muyi hakan ba?

Ni ban amince da abinda Sarki Sanusi ya ce ba a kan wannan lamarin.

DUBA WANNAN: Ban bada umarnin kama wanda ya siya tsohon layi na ba - Hanan Buhari

Allah ne ya kaddara wa iyaye haifar yaran da suka haifa kuma nauyi ya rataya a kansu su musu tarbiyya su kuma daura su kan turba mai kyau.

Sun zabi almajiranci. Suna son 'ya'yansu su koyi karatun Kurani, shin hakan laifi ne?

Su ma 'yan Najeriya ne kuma suna da ikon zaban abinda suke so.

Idan ba munafinci ba, wasu daga cikin ku kuna tura 'ya'yan ku makarantun boko ta Nursery tun suna shekara daya amma kuna sukan almajiranci. Ku na tura 'ya'yan ku makarantun kwana amma kuna fadawa iyayen almajirai su dena tura 'ya'yansu wasu garuruwan. Ta yaya ku ke so su samu ilimi?

Galibin ku ba ku fahimta bane.

Ku na dauka bara a titi shine almajiranci. Bara a titi baya cikin tsarin karatun almajiranci na ainihi.

Idan har gwamnati za ta iya samar wa daliban makarantun kwana abinci, me zai hana a yi wa almajirai hakan? Su ba 'yan Najeriya bane?

Almajirai na ainihi ba su bara. Bara wata mummunan dabi'a ce da wasu suka shigar da ita cikn tsarin almajiranci kuma ya kamata su canja abin ba wai hana almajiranci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel