Gwamnati na Shirin Janye Harajin Shigo da Kaya, Ana sa Ran Saukar Farashin Abinci
- Rahotanni na nuna cewa gwamnatin tarayya na shirin dakatar da karbar haraji kan wasu muhimman kayayyaki da ake shigowa da su kasar nan domin saukaka hauhawar farashi
- Daga kayayyakin da za a dagewa haraji na watanni shida akwai kayan abinci, magunguna, irin dashe, kayan abincin kaji, fulawa, da makamantansu domin yakar tashin farashi
- Akwai wasu nau'i na kayayyaki da su kuma za a cirewa harajin VAT na tsawon shekara guda kamar kayan sarrafa kayayyaki, iskar gas din da ababe hawa ke amfani da shi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Yayin da ake fama da tsadar kayan abinci, gwamnatin tarayya na shirin dakatar da harajin shigo da wasu muhimman kaya cikin kasar nan.
Matakin ya biyo bayan hauhawar farashi da 'yan Najeriya ke ta kokawa a kai, musamman tun bayan hawan mulkin Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2023.
Wani rahoton da Bloomberg ta wallafa ya nuna cewa daga kayan da za a dakatar da karbar haraji a kai akwai kayan abinci, magunguna da muhimman kayan amfanin yau da kullum.
Waɗanne kaya za a cirewa haraji?
A takardar da Punch ta gani an mika ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanyawa hannu, za a ɗage karbar harajin na tsawon watanni shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga kayan abinci da magunguna, sauran kayan da za a dage karbar haraji a kansu sun haɗa da taki saboda amfanin manoma, irin dashe, kayan abincin kaji, fulawa da hatsi.
Dokar za shugaban ya kamata ya rattabawa hannu tun a watan Afrilu zai ba babban bankin kasa (CBN) damar ba bangaren manoma da masu hada magunguna bashi mai saukin ruwa.
Gwamnati za ta jingine harajin VAT
Bayanan da ke kunshe a jikin takardar sun nuna yiwuwar jingine harajin VAT daga wasu kayan amfani.
Daga kayan da ake sa ran za a daukewa harajin na tsawon shekara ɗaya akwai man gas da ababen hawa ke amfani da shi. Sai kayan da za a sarrafa wajen hada kaya, sai taliya, hasken wuta, kudin mota, kayan noma da magunguna.
'Har yanzu ana biyan tallafin fetur,' Atiku
A baya mun kawo muku labarin yadda tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan yaudarar jama'a.
Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin PDP ya ce har yanzu ana biyan kudin tallafin man fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng