Dhul Hijjah: Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa Kan Ranakun Hawa Arfah da Babbar Sallah
- Hukumomin ƙasa mai tsarki sun buƙaci Musulmai su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah idan Allah ya kaimu gobe Alhamis, 29 ga Dhul Qa'adah
- A wata sanarwa da kotun ƙolin Saudiyyya ta fitar ranar Laraba, ta ce ganin watan zai tabbatar da ranakun aikin hajji da suka haɗa da Arfah da Babbar Sallah
- A ranar 10 ga watan Dhul Hijjah Musulmi ke gudanar da Babbar Sallah, ɗaya daga cikin ibada masu muhimmanci a Addinin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun buƙaci al'ummar musulmi na ƙasar su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah gobe Alhamis.
Watan Dhul Hijja wanda ya kasance wata na 12 a jerin kalandar addinin Musulunci, shi ne watan da Musulman duniya ke yin Sallar Layya.
Ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024 za ta kasance daidai da 29 ga watan Dhul Qa'ada, bisa haka hukumomin Saudiyya suka nemi a fara duban watan 12.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ƙolin saudiyya ce ta bayyana haka a wata sanarwa da shafin Inside Haramain ya wallafa a manhajar X wadda aka fi sani da Twitter.
Saudiyya za ta tabbatar da ranar Sallah
Sanarwan ta ce:
"Kotun koli na kira ga ɗaukacin Musulmin ƙasar Saudi Arabia su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah daga gobe Alhamis, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1445AH daidai da 6 ga watan Yunin 2024.
"Ganin jinjirin watan ne zai tabbatar da ranakun aikin hajji da suka haɗa da ranar hawan Arfah da kuma ranar babbar Sallah."
Sanarwar ta buƙaci waɗanda za su iya duban watan da idanuwansu ko na'urar hangen nesa da su kai rahoton ganin watan ga kotu mafi kusa da su.
Musulmai na gudanar da idin Babbar Sallah ne ranar 10 ga watan Dhul Hijjah na kowace shekara, yayin da Alhazai ke hawan Arfah ranar 9 ga watan 12 a Musulunci.
Maniyyata miliyan 1 sun isa Saudiyya
A wani rahoton kuma Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa kimanin maniyyata ‘yan kasashen waje miliyan daya ne suka isa aikin hajjin 2024.
Akalla musulmai miliyan biyu ne ake sa ran za su je aikin hajjin bana a Makkah inda ake sa tsammanin 65,000 daga Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng