Shaguna Sun Kone Bayan Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Katako

Shaguna Sun Kone Bayan Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Katako

  • Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar Katako da ke kan titin Kenyatta a Uwani cikin birnin Enugu, babban birnin jihar Enugu
  • Gobarar wacce ta tashi cikin dare ta ƙona shaguna biyar da ke cikin kasuwar kafin a yi nasarar kashe ta
  • Jami'an hukumar kashe gobara ne suka kawo agajin gaggawa inda suka kashe gobarar ba tare da ta yaɗu zuwa sauran sassan kasuwar ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - An samu tashin gobara a kasuwar Katako da ke kan titin Kenyatta, a Uwani cikin birnin Enugu.

Gobarar wacce ta tashi a ranar Talata, ta lalata aƙalla shaguna biyar da ke cikin kasuwar.

Gobara ta tashi a kasuwar Katako Enugu
Gobara ta kona shaguna biyar a kasuwar Katako a Enugu Hoto: @fedfireng
Asali: Facebook

Jami'an kashe gobara sun kai ɗauki

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa cikin gaggawa jami'an hukumar kashe gobara suka kawo agajin gaggawa a kasuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙoƙarin da suka yi wajen kashe gobarar ya sanya ba ta yaɗu zuwa sauran sassan da ke cikin kasuwar katakon ba, rahoton PM News ya tabbatar.

Wani ma’aikacin kashe gobara da ya so a sakaya sunansa ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:45 na dare kuma nan take suka garzaya zuwa wajen.

Ya ce sun yi nasarar kashe gobarar ba tare da ta yaɗu zuwa sauran sassan kasuwar ba.

"Kusan shaguna biyar ne gobarar ta shafa a wannan babbar kasuwar. Ba zan iya cewa komai kan faruwar lamarin ba kasancewar ba ni ba ne shugaban hukumar kashe gobara."

- Wani ma'aikacin kashe gobara

Yaushe gobarar ta tashi?

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka a Bauchi bayan barkewar ruwan sama kamar da bakin kwarya

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Joe, ya bayyana cewa ya ga tashin gobarar ne bayan ƙungiyar ƙwadago ta dakatar da yajin aikin da take yi a faɗin ƙasar nan.

A cewarsa, wasu mutanen da ke makwabtaka da wajen sun garzaya zuwa kasuwar inda a cikin ƴan mintoci kaɗan jami’an kashe gobara suka iso suka kashe gobarar.

"Na godewa Allah da jami'an hukumar kashe gobara suka kawo agajin gaggawa, da ba domin hakan ba, da an yi mummunar ɓarna."

- Joe

Gobara ta hallaka mutane a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana matsalolin tashin gobarar da ta fuskanta da asarar da mutane suka yi cikin watan Mayun 2024.

Hukumar ta ce tashin gobara daban-daban da suka faru ya yi ajalin mutum takwas tare da lalata kadarorin da kudinsu ya kai Naira miliyan 31,650,700.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel