“Za a Tuna da Kai”: Tinubu Ya Karrama Babban Marubucin Najeriya, Wole Soyinka
- Shugaba Bola Tinubu ya karrama babban marubucin Najeriya, Wole Soyinka ta hanyar sanya wa sabuwar hanyar N20 sunan sa
- An kaddamar da titin N20 da ya taso daga 'Northern Parkway' zuwa wajen sha tale-talen arewacin Abuja (ONEX) a ranar Talata
- Tinubu ya kambama Farfesa Wole Soyinka wanda ya ce ya jawo wa Najeriya farin jini, da kuma samun tarin yabo a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa sabuwar hanyar N20 da aka kaddamar a Abuja sunan Farfesa Wole Soyinka domin karrama babban marubucin kasar.
Shugaban kasar ya kaddamar da titin da ya taso daga 'Northern Parkway' zuwa wajen sha tale-talen arewacin Abuja (ONEX) a ranar Talata.
Bola Tinubu ya bugi kirji da titin N20
Titin na N20 na daya daga cikin manyan hanyoyin da suka hada da ONEX da wajen sha tale-talen kudancin Abuja (OSEX) ta hanyoyi shiga daban-daban, in ji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, hanyar za ta inganta zirga-zirgar ababen hawa daga gundumomin Mabushi, Katampe, Jahi, da Kado.
Jaridar The Nation ta ruwaito Tinubu ya bayyana aikin hanyar a matsayin wata shaida ta nuna nasarar gwamnatinsa na kawo sauyi a kowane bangare na kasar nan.
Tinubu ya karrama Wole Soyinka
Shugaban kasar a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da titin ya bayyana sunan titin na N20 a matsayin 'hanyar Wole Soyinka'.
Shugaba Tinubu ya ce:
“Bari in ce shawarar sanya sunan wannan titin na N20 a matsayin 'hanyar Wole Soyinka' ta samu karbuwa sosai. Shi ne babban marubucinmu, kuma wanda ya ci kyautar 'Nobel'.
“Ya jawo wa Najeriya farin jini, da kuma samun tarin yabo a duniya wanda ba za a manta da shi ba.Mun yarda da wannan shawarar a madadin al'ummar tarayyar Najeriya."
Kaduna: Amarya ta datse mazakutar ango
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata amarya, Habiba Ibrahim ta datse mazakutar angonta Salisu Idris yana barci a garin Kudan da ke jihar Kaduna.
Salisu ya bayyana kaduwarsa kan wannan mummunar aika-aika da Habiba ta yi masa yana mai cewa babu wani sabani da ya shiga tsakaninsu a iya saninsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng