Tashar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna za ta samu sabbin jiragen kasa a ranar Alhamis din nan - Inji Buhari

Tashar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna za ta samu sabbin jiragen kasa a ranar Alhamis din nan - Inji Buhari

- Jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna zasu dauka kimani fasinjoji miliyan daya a kowace shekara

- Shugaba Buhari ya ce za a shigo da karin wasu sabbin jiragen kasa a ranar Alhamis din nan

- Shugaban kasa ya bayyana cewa a cikin 'yan shekarun nan, dukkanin biranen Najeriya za a haɗa su ta hanyar tsari na zamani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a jawabinsa na sakon sabuwar shekara cewa gwamnatinsa za ta kara inganta aikin jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna da wasu sabbin jiragen kasa a ranar Alhamis din nan wanda zai iya daukar kimani mutane miliyan daya a kowace shekara.

Legit.ng ta tattaro cewa, shugaban ya sanar da hakan ne a cikin wani jawabi ga al'ummar kasar a ranar Litinin, 1 ga watan Janairu don nuna murnar sabon shekara ta 2018.

Ya kuma sanar da cewa za a kammala tattaunawa a farkon shekarar 2018 aikin hanyar jiragen kasa na Fatakwal zuwa Maiduguri wanda zai hada Aba, Owerri, Umuahia, Enugu, Awka, Abakaliki, Makurdi, Lafia, Jos, Bauchi, Gombe, Yola da kuma Damaturu.

Za a inganta zirga-zirgar Abuja zuwa Kaduna da wasu sabbin jiragen kasa a ranar Alhamis din nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ya ce hanyar jiragen kasa wanda ta hada birnin Abuja zuwa Itakpe zai shiga Baro kuma ya ƙare a Warri tare da gina sabon tashar jiragen ruwa a Warri.

KU KARANTA: Babban Bankin Duniya ya yabawa Gwamnatin Najeriya na damawa da ‘Yan kasuwa

A cewar shugaban, tattaunawar ta yi nisa game da gine-ginen hanyoyin jiragen kasa, wanda za ta fara daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar ta wuce Kazaure, Daura, Katsina, Jibia sa a nan Maradi.

Na biyu kuma daga Lagas zuwa Calabar, wanda zai hada Ore, Benin, Agbor, Asaba, Onitsha, Sapele, Ughelli, Warri, Yenagoa, Otuoke, Fatakwal, Aba, Uyo da kuma Calabar.

"A cikin 'yan shekarun nan, dukkanin waɗannan biranen Najeriya za a haɗa su ta hanyar tsarin zamani, wannan shirin zai taimaka wajen inganta tattalin arziki da kuma rayuwar al’ummar kasar", in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel