Tsautsayi Ya Gitta, Allah Ya Yiwa Babban Jami'in Ɗan Sanda Rasuwa Yana Zaune a Ofis

Tsautsayi Ya Gitta, Allah Ya Yiwa Babban Jami'in Ɗan Sanda Rasuwa Yana Zaune a Ofis

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta shiga jimami yayin da babban jami'inta ya riga mu gidan gaskiya a ofishinsa a Abuja
  • Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DSP Abubakar Muhammad Guri ya rasu jim kaɗan bayan ya shiga ofis a hedkwatar ƴan sanda
  • Har kawo yanzu rundunar ƴan sandan Najeriya ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan wannan lamarin mara daɗi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DCP Abubakar Muhammad Guri, ya riga mu gidan gaskiya a ofishinsa da ke hedkwata a Abuja.

Rahotanni da muka samu ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024 sun nuna cewa DCP Abubakar ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Abubuwan da aka Amince da su a taron Gwamnatin Tinubu da ƴan ƙwadago

DCP Guri da IGP Kayode.
Allah ya yiwa DCP Abubakar Guri rasuwa a hedkwatar ƴan sanda. Mun sa hoton IGP ne domin nuni kaɗai Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda 'dan sanda DCP Abubakar ya rasu

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, marigayi DCP ya gamu da ajalinsa a zaune a kan kujera a ofishinsa da ke hedkwatar ƴan sanda ta ƙasa a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ya faɗi ƙasa, jami'an da ke wurin sun yi hanzarin kai shi asibiti domin ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.

An tattaro cewa kafin rasuwarsa, DCP Abubakar ya fito wurin aiki cikin ƙoshin lafiya kuma har gaisawa ya yi da wasu jami'an ƴan sanda sashen Mopol a wannan rana.

Wata majiya ta ce:

"Wasu jami'an ƴan sanda sun yi gaggawar ɗaukarsa zuwa asbiti kuma tun kafin su karasa ya rasu."

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar ƴan sanda ba ta faɗi wani dalili a hukumance wanda ya zama sanadin mutuwar jami’in ba.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi umarnin kungiyoyin NLC da TUC

Menene ya zama ajalin DCP Guri?

Sai dai wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa mutuwar babban jami’in ba za ta rasa nasaba da ciwon zuciya ba, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Majiyar ta ƙara da cewa ba shi kaɗai ba, ‘yan sanda da dama irin haka ta faru da su saboda gajiyar da suke fuskanta, domin kuwa suna aiki dare da rana ba tare da hutu ba.

An kama ɗan bindiga a Zaria

A wani rahoton kuma 'yan sanda sun kama wani dattijo ɗan shekara 70 a duniya wanda ake zargin ɗan bindiga ne a Zariya da ke jihar Kaduna.

Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa dattijon ya fara ba da haɗin kai domin kama dukkan waɗanda ke taimaka masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel