Shugaba Tinubu Ya Shiga Muhimmin Taro Kan Mafi Karancin Albashi, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da wakilan tawagar gwamnatin tarayya a kwamitin tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi
- Shugaban ƙasan ya shiga ganawar ne da tawagar a fadarsa da ke Aso Rock Villa a cikin birnin tarayya Abuja
- Ganawar ta su na zuwa ne bayan ƴan kwadago sun sassauta yajin aikin da suke yi kan mafi ƙarancin albashin da za a biya ma'aikata a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gana da wakilan tawagar gwamnatin tarayya a kwamitin da ke kula da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
Shugaba Tinubu ya gana da tawagar wakilan na gwamnatin tarayya ne a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock a Abuja.
Tinubu ya gana da wakilan gwamnati
Ganawar da shugaban ƙasar ya yi da wakilan gwamnati kan mafi ƙarancin albashin na zuwa ne kimanin sa’a ɗaya kafin a koma tattaunawa tsakanin ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin tarayya, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka gana da shugaban ƙasar sun hada da ministan kuɗi da tattalin arziƙi, Wale Edun, ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Sauran sun haɗa da ƙaramar ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Nkeiruka Onyejeocha da kuma shugaban kamfanin man fetur na ƙasa NNPC, Mele Kyari.
Menene dalilin ganawa da Tinubu?
Taron dai ba zai rasa nasaba da yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon suka fara yi kan rashin kammala tattaunawa dangane da sabon mafi ƙarancin albashi da kuma buƙatar sauya ƙarin kuɗin wutar lantarki.
Ana sa ran tawagar za ta yiwa shugaban ƙasa bayani kan tattaunawar da ake yi da sanya shi ya yi alƙawarin yin ƙari kan mafi ƙarancin albashin bayan ƴan ƙwadago sun ƙi amincewa da tayin N60,000.
Abin da ya kamata gwamnati biya ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa Daniel Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnatin tarayya ta riƙa biyan ma'aikata N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Daniel Bwala ya bayyana cewa tayin da gwamnati ta yi na biyan N60,000 ya yi kaɗan duba da yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng