Bayan Tsawon Kwanaki 75, Sanata Abdul Ningi Ya Koma Zaman Majalisa
- Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ya koma halartar zaman majalisa a ranar Talata, 4 ga watan Yuni
- Sanatan ya koma zaman majalisar ne bayan afuwar da aka yi masa daga dakatar da shi daga majalisar a ranar 12, ga watan Maris 2024
- A makon da ya gabata ne dai majalisar ta yi masa afuwa kan dakatarwar da aka yi masa bayan ya yi zargin an yi cushe a kasafin kuɗin 2024
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi, a ranar Talata, ya koma bakin aiki a majalisar dattawa.
Sanatan ya shafe kwanaki 75 ba shi a cikin majalisa biyo bayan dakatarwar da aka yi masa.
Majalisa ta yiwa Sanata Ningi afuwa
Majalisar dattawa ta yi masa afuwa kuma ta buƙaci ya dawo majalisa wanda hakan ya kawo ƙarshen dakatarwar da aka yi masa daga ranar 12 ga watan Maris, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A makon da ya gabata, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Abba Moro ya gabatar da ƙudirin neman a yiwa Sanata Abdul Ningi afuwa a dawo da shi majalisa.
Shugaban majalisa ya amince a maido Ningi
Daga baya shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da dawo da Abdul Ningi ba tare da sanya wani sharaɗi ba bayan roƙon da wasu ƴan majalisar suka yi.
Dakatarwar da aka yi masa dai ta biyo bayan zargin da ya yi cewa an yi cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024.
Sanata Abdul Ningi ya yi zargin cewa majalisar ta amince da kasafin kuɗin N25tr yayin da gwamnatin tarayya ke amfani da kasafin kuɗin N28.7tr.
Abdul Ningi ya koma majalisar dattawa
Domin nuna farin cikin dawowarsa majalisar dattawa, Sanata Ningi na daga cikin sanatocin da suka fara isa harabar majalisar dokoki ta ƙasa ranar Talata.
Sanata Ningi, tare da wasu Sanatoci irinsu Suleiman Kawu Sumaila (NNPP, Kano ta Kudu), da Aminu Waziri Tambuwal (PDP, Sokoto ta Kudu), sun shigo majalisar da misalin ƙarfe 10:40 na safe, mintuna 20 kafin lokacin fara zaman majalisar.
Batun dakatar da Sanata Abdul Ningi
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta bayyana cewa da yiwuwar ta sake duba matakin da ta ɗauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya.
An dakatar da Sanata Ningi na tsawon watanni uku saboda iƙirarin da ya yi cewa majalisar tarayya ta yi cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng