Kungiyar Ƙwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 1

Kungiyar Ƙwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 1

  • Kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suke yi a fadin kasar na tsawon mako guda
  • Hakan ya biyo bayan wani taro na musamman da majalisar zartarwar kungiyoyin ta kasa da suka yi a safiyar Talata a Abuja
  • Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ne ya sanar da tsagaita yajin jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyoyin ƙwadagon Najeriya na NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin sai baba ta gani da suka fara a jiya Litinin a faɗin ƙasar.

'Yan kwadago sun janye yajin aiki
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suka shiga. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Facebook

'Yan kwadago sun janye yajin aiki

NLC da TUC sun tsagaita yajin aikin ne na mako ɗaya rak, a kokarin da suke yi na ganin su da gwamnatin tarayya an cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana yadda yajin aikin 'yan NLC zai kara jefa al'umma a wahala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna, shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ne ya sanar da tsagaita yajin aikin a ranar Talata a Abuja.

Wannan ya biyo bayan wani taron majalisar zartarwar kungiyoyin da ya aka yi a Abuja. Osifo ya ce za su fitar da sanarwar bayan taro nan gaba kaɗan, in ji rahoton Daily Trust.

Gwamnati ta gana da NLC, TUC

Bayan rufe bankuna, makarantu da ofisoshin gwamnati da dai sauran su, gwamnatin tarayya ta gayyaci shugabannin kwadago zuwa wani taro a ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

A karshen taron a daren ranar Litinin, gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin da zai haura N60,000.

Dangane da zaman taron, kwamitin kayyade mafi ƙarancin albashi da gwamnatin tarayya ta kafa zai rika yin zama a kullum har na mako guda domin kammala rahotonsa.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya hana jigilar Alhazai zuwa ƙasa mai tsarki? NAHCON ta faɗi gaskiya

CBN zai kwace lasisin bankuna 3?

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya karyata wani rahoto da ake yadawa a yanar gizo cewa zai kwace lasisin bankin Unity, Polaris da Keystone.

Babban bankin ya ce wannan labarin karya ne tsagoronta domin ba shi da wani shiri na kwace lasisin bankunan uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.