NLC Ta Fitar da Sanarwa Kan Makomar Yajin Aiki Bayan Zama da Gwamnati, Ta Yi Gargadi
- Kungiyar kwadago a Najeriya (NLC) ta fitar da sanarwa da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni kan ci gaba da yajin aiki
- Kungiyar ta tabbatar da cewa za a ci gaba da yajin aiki har sai bayan tattaunawa da za ta yi da 'ya 'yanta a rassan kasar
- Legit Hausa ta tattauna da wasu ma'aikata kan wannan sanarwa da NLC ta fitar kan yakin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta NLC ta magantu bayan tattaunawar da ta yi da gwamnati kan yajin aiki a Najeriya.
Kungiyar ta ce a yau za a ci gaba da yajin aiki har sai an ji daga gare ta bayan ganawa da suka yi da Gwamnatin Tarayya.
Yajin aiki: Sanarwar da NLC ta fitar
NLC ta bayyana haka ne da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni a shafinta na X inda ta ce a ci gaba da zama a gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da zaman da aka yi a jiya Litinin 3 ga watan Yuni da gwamnati, kungiyar ta ce za ta yi duba kan yarjejeniyar da aka yi a ganawar a jiya Litinin.
Kungiyar ta bukaci ci gaba da yajin aikin har sai ta fitar sanarwa bayan ganawa a yau Talata 4 ga watan Yuni.
NLC ta bukaci cigaba da zaman gida
"Har sai kun ji daga gare mu a ganawar da za mu yi a yau Talata 4 ga watan Yuni, za a ci gaba da yajin aiki."
- NLC
Legit Hausa ta tattauna da wasu ma'aikata kan wannan sanarwa da NLC ta fitar kan yakin aiki.
Umar Abdulkadir a ma'aikatar ilimi daga tushe ya ce matakin NLC ya yi dai-dai saboda hakan ne kadai gwamnatin ke fahimta.
Bello Aliyu da ke ma'aikatar ilimi ya ce babban matsalar ko an samu daidaito kan mafi karancin albashi gwamnonin ne matsalar ba Gwamnatin Tarayya ba.
"Har yanzu akwai gwamnatocin jihohi da ba su iya biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi."
"Duk matsayar da aka samu gwamnoni ne za su fara kawo matsala wurin gaza biyan albashi."
- Bello Aliyu
NLC ta tattauna da Gwamnatin Tarayya
A wani labarin, kun ji cewa an ƙarkare taron gaggawa da Gwamnatin Tarayya ta kira ƴan kwadago kan yajin aikin da aka fara a makon nan.
Idan ba ku manta ba muna kawo rahoton cewa shugabannin ƴan kwadago sun isa ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya domin shiga taron gaggawa da aka gayyace su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng