An Bukaci Kungiyar Kwadago Ta Dakatar da Yajin Aiki Saboda Jigilar Mahajjata

An Bukaci Kungiyar Kwadago Ta Dakatar da Yajin Aiki Saboda Jigilar Mahajjata

  • Kungiyar masu jigilar mahajjata ta kasa (AHOUN) ta yi kira na musamman ga kungiyar kwadago kan yajin aiki da ta shiga
  • Cikin sakon ta kungiyar ta wallafa ta nuna cewa duk da muhimmancin yajin aikin ga rayuwar ma'aikata, yazo a lokacin da bai dace ba
  • Ta kuma bayyana yadda yajin aikin zai shafi rayuwar al'ummar Musulmi a kan harkokin ibada wanda hakan koma baya ne

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar masu jigilar mahajjata ta kasa (AHOUN) ta yi kira ga kungiyar kwadago kan duba janye yajin aikin da ta fara.

Shugaban kungiyar na kasa, Abdullateef Ekundayo Yusuf ne ya yi kiran ga kungiyar kwadago bayan yajin aikin ya jawo tsaiko ga jigilar mahajjata.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC: Kungiyar MURIC ta tona abin da ya faru da jirgin maniyyatan aikin hajji

Mahajjata
An bukaci kungiyar kawadago ta hakura da yajin aiki saboda aikin Hajji. Hoto: NLC Headquaters|Inside the Haramain
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar AHUON ta ce 'yan kwadago suna da dalilan shiga yajin aikin amma kuma tsayar da ayyuka ibada ma abin dubawa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran shugaban AHOUN ga NLC kan mahajjata

Shugaban AHUON, Abdullateef Ekundayo Yusuf ya ce aikin hajji yana cikin rukunan Musulunci da ake so kowane Musulmi ya yi.

Sannan ya kara da cewa wasu daga cikin maniyyatan sun dauki shekaru suna tara kudin aikin Hajji, rahoton Punch.

Saboda haka ya yi kira ga yan kwadago su duba yiwuwar dakatar da yajin aikin har sai an gama jigilar mahajjata.

Asarar da yajin aikin zai jawowa mahajatta

Har ila yau shugaban kungiyar ya bayyana cewa mahajjatan sun kammala biyan kudin jirgi domin tafiya Hajji.

Sun kuma kammala biyan kudi domin kama musu masauki, zirga-zirga da kudin abinci a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta hana Alkalai zaman kotu saboda yajin aiki a Abuja

A karkashin haka ya ce idan ba a janye yajin aikin ba zai haifar da asarar dukiya mai yawa ga 'yan Najeriya.

An roki NLC ta janye yajin aiki

A wani rahoton, kun ji cewa a yayin da kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki a yau Litinin, mutane sun fara bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin.

Tsohon daraktan kafar yada labaran VON, Osita Okechukwu ya ba kungiyar kwadago hakuri ta janye yajin aikin da ta shiga domin kawo sauki a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng