Kungiyar Kwadago Ta Hana Alkalai Zaman Kotu Saboda Yajin Aiki a Abuja
- Ma'aikatan kotu a babban birnin tarayya Abuja sun hana alkalai da lauyoyi gudanar da aiki a yau Litinin, 3 ga watan Yuni
- Ma'aikatan sun bayyana cewa za su hana cigaba da sauraron kara a kotunan Abuja har sai kungiyar kwadago ta janye yajin aiki
- Yayin da kungiyar kwadago ta fara yajin aiki a yau ta umurci dukkan ma'aikata su rufe wuraren aiki a Najeriya sai baba ta gani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Kungiyar ma'aikatan kotu (JASUN) ta hana zaman kotu a birnin tarayya Abuja biyo bayan fara yajin aikin 'yan kwadago.
A safiyar yau Litinin ne kungiyar ta kulle kotuna domin hana alkalai, lauyoyi da masu ƙara shiga su gabatar da shari'a.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar JASUN ta dauki matakin ne a kusan dukkan kotunan da suke birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda babbar kotun kasa ta kasance
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan kungiyar JASUN sun yi zaman dirshan yayin da suka kulle babban kotun kasa da ke Abuja a yau.
Ma'aikata sun hana alkalai, lauyoyi, masu shigar da ƙara, masu ziyara da 'yan jarida shiga kotun domin yin ayyuka, rahoton Vanguard.
Yadda kotun daukaka kara ta kasance
Ma'ajin JASUN, Muhammad Danjuma-Yusuf ya ce kotuna 20 da suke karkashin kotun daukaka kara duk an kulle su a yau.
Muhammad Danjuma-Yusuf ya ce ba su bar kowa ya shiga kotunan ba kuma haka lamarin zai cigaba har sai kungiyar kwadago ta janye yajin aiki.
Yajin-aiki: Dalilin rufe kotuna a Abuja
Shugaban kungiyar JASUN reshen Abuja, Samuel Ikpatt ya ce kungiyar ta bi umurnin kungiyar kwadago ne wajen rufe kotunan a yau.
Samuel Ikpatt ya ce ba su bar wani ya shiga kotun domin aiki ba kuma sun tabbatar da haka a dukkan kotunan da ke birnin Abuja.
'Yan sanda sun gargadi NLC
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya ta gargadi kungiyar kwadago kan shiga yajin aiki da ta yi a yau Litinin.
Rundunar 'yan sandan ta ce yajin aikin ba bisa doka da oda yake ba kuma zai iya kai ga tayar da fitina a Najeriya saboda haka ya kamata kungiyar kwadago ta gaggauta janye sa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng