Yajin Aiki: ’Yan Ƙwadago Sun Fatattaki Jama’a Daga Cikin Wani Bankin Legas

Yajin Aiki: ’Yan Ƙwadago Sun Fatattaki Jama’a Daga Cikin Wani Bankin Legas

  • Kungiyar 'yan kwadago ta NLC reshen jihar Legas sun kai samame wani bankin Polaris da ke Alausa inda suka fatattaki jama'ar da ke ciki
  • 'Yan kwadagon sun dura bankin tare da fatattakar abokan hulda domin tabbatar da bin umarnin kungiyar na shiga yajin aiki
  • A jihar Imo ma kungiyar kwadago ta NLC ta rufe bankuna, sakatariyar jiha da ta tarayya bisa bin umarnin uwar kungiyar ta kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - An kwashi 'yan kallo a wani bankin Polaris da ke jihar Legas a ranar Litinin bayan da mambobin kungiyar kwadago na NLC suka dura bankin.

'Yan kwadago sun rufe banki a Legas
Yajin Aiki: 'Yan kwadago sun rufe banki tare da korar jama'a a Legas. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

'Yan kwadagon sun dura bankin tare da fatattakar abokan hulda domin tabbatar da bin umarnin kungiyar na shiga yajin aikin gama gari.

Kara karanta wannan

NLC ta koro dalibai da abokan huldar bankuna saboda yajin aiki a Kaduna

'Yan kwadago sun dura bankin Polaris

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan kwadagon ba su bar bankin ba sai da suka tabbatar sun fatattaki kowa tare da rufe bankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kwadago sun rufe sakatariyar jihar Legas da ke Alausa domin tabbatar da yajin aikin da suka shiga.

A yayin da su ke rangadi a fadin jihar ne 'yan kwadagon bisa jagorancin Kwamred Funmi Sessi suka kutsa bankin na Polaris da ke Alausa.

NLC ta rufe bankuna da ma'aikatu

Jaridar Vanguard ta ruwaito kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Imo ta rufe bankuna, sakatariyar jiha da ta tarayya bisa bin umarnin uwar kungiya na shiga yajin aiki.

Sakataren yada labarai na NLC na jihar, Ifeanyi Nwanguma, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin yajin aikin.

Abuja: NLC ta rufe gin majalisar tarayya

Kara karanta wannan

Yajin aiki: 'Yan ƙwadago sun dura ginin majalisar tarayya, sun katse wuta da ruwa

A wani labarin, mun ruwaito kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), ta rufe kofar shiga ginin da wasu motocin bas guda biyu.

PASAN da ke bin umarnin kungiyar NLC ta kuma katse wuta da ruwan ginin majalisun biyu, domin tabbatar da an bi umarnin shiga yajin aiki a fadin kasar.

Yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da daukar zafi a babban birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.