Yajin Aiki: ’Yan Ƙwadago Sun Dura Ginin Majalisar Tarayya, Sun Katse Wuta da Ruwa

Yajin Aiki: ’Yan Ƙwadago Sun Dura Ginin Majalisar Tarayya, Sun Katse Wuta da Ruwa

  • Kungiyar kwadago ta rufe majalisar dokokin kasar nan tare da katse ruwa da wuta na ginin a yajin aikin da 'yan kwadagon suka fara
  • An ruwaito kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), ta rufe kofar shiga ginin da wasu motocin bas guda biyu
  • Yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da daukar zafi a babban birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mambobin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), reshen kungiyar NLC, sun rufe majalisar dokokin kasar, a yajin aikin da 'yan kwadagon suka fara.

A safiyar yau muka ruwaito yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da daukar zafi a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: 'Yan ƙwadago sun fatattaki jama'a daga cikin wani bankin Legas

'Yan kwadago sun dura ginin majalisar dattawa da na wakilai
Yajin aiki: ’Yan kwadago sun datse ruwa da wuta na ginin majalisar tarayya. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Wakilin jaridar Daily Trust da ya je majalisar dokokin kasar domin duba halin da ake ciki ya tarar PASAN ta rufe kofar shiga ginin da wasu manyan motocin bas guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan kwadago sun gana da 'yan majalisa

Kungiyoyin kwadago dai sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a yau bayan kin amincewar da gwamnatin tarayya na kara mafi karancin albashi zuwa sama da N60,000.

'Yan kwadagon masu neman N494,000 sun yi wata ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar da manyan jami’an gwamnati a jiya Lahadi kan shiga yajin aikin.

Sai dai taron ya tashi ba tare da an samu wata nasara ba bayan da shugabanin kungiyoyin kwadagon sun ce babu gudu babu ja da baya kan shiga yajin aiki.

'Yan kwadago sun rufe ma'aikatun tarayya

An ce kungiyar kwadago ta datse wutar lantarki da ruwan sha ga wasu gine-ginen majalisar dattawa da na wakilai.

Kara karanta wannan

NLC ta koro dalibai da abokan huldar bankuna saboda yajin aiki a Kaduna

Mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista a Abuja.

NLC ta rufe tashar wutar lantarki ta kasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da rarraba wutar lantarki ta Najeriya (TCN) ta ce kungiyar ma’aikatanta ta rufe tashar wutar lantarki ta kasa.

Babban manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin.ya ce lamarin ya haifar da katsewar wuta a fadin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel