Yajin Aikin Kungiyoyin Ƙwadago Ya Ɗauki Zafi, an Rufe Ofishin Ministan Abuja

Yajin Aikin Kungiyoyin Ƙwadago Ya Ɗauki Zafi, an Rufe Ofishin Ministan Abuja

  • Kungiyoyin kwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista a Abuja
  • Ginin ma'aikatar dai yana dauke da ofishin ministan Abuja, Nyesom Wike da na ministan noma, Sanata Abubakar Kyari
  • Shugabar kungiyar kwadago ta JUAC, Kwamred Rifkatu Lortyer, ta sha alwashin ci gaba da rufe ginin har sai an biya bukatunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da daukar zafi a babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyoyin kwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista, inda a ka hana ma’aikatan shiga.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: 'Yan ƙwadago sun fatattaki jama'a daga cikin wani bankin Legas

Zanga-zangar 'yan kwadago a Abuja
'Yan kwadago sun rufe ginin ofishin ministan Abuja. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Getty Images

An rufe ginin ofishin ministan Abuja

Jaridar The Nation ta ruwaito 'yan kwadago na hukumar kula da babban birnin tarayya (FCTA) da na hukumar FCDA da kuma kungiyar kwadago ta hadin guiwa (JUAC) ne suka rufe ginin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ga ma’aikatan ma'aikatar suna shawagi a kusa da kofar yayin da shugabannin kwadago suka tilasta bin umarnin “babu shiga-babu fita.”

Shugabar JUAC, Comrade Rifkatu Lortyer, ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin har sai an biya wa 'yan kwadago bukatunsu.

Kungiyar kwadago ta gargadi ma'aikata

Ta shawarci ma’aikatan hukumomin FCTA da FCDA da su zauna a gidajensu domin bin umarnin NLC da TUC in ji rahoton jaridar Vanguard.

Ginin ma'aikatar dai yana dauke da ofishin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da takwaransa na harkokin noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: 'Yan ƙwadago sun dura ginin majalisar tarayya, sun katse wuta da ruwa

An ruwaito cewa jami’an tsaro a yanzu haka suna kofar shiga hukumomin FCTA da FCDA domin tabbatar da tsaro.

CBN ya kwace lasisin bankin Heritage

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya kwace lasisin bankin Heritage tare da mika ikonsa ga hukumar inshorar ajiyar kudade.

CBN ya kwace lasisin bankin Heritage ne saboda ya karya sashe na 12 (1) na dokar BOFIA 2020 da kuma gaza samun wadatattun kudaden gudanar da ayyukansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel