Kotu Na Shirin Yanke Hukunci Tsakanin Tsohon Ministan Buhari da Surukarsa

Kotu Na Shirin Yanke Hukunci Tsakanin Tsohon Ministan Buhari da Surukarsa

  • Bayan dadadden rikici da ke tsakanin tsohon minista, Goeffrey Onyeama da surukarsa kotu na daf da yanke hukunci
  • Tsohon ministan na rikici da surukarsa, Lilian Onoh kan zargin cin hanci da rashawa da ta yi masa a lokacin da yake minista
  • Dukkan bangarorin sun bukaci kotun ta sa a biya su tara saboda bata suna da tayar da hankali da suka samu saboda shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kotu na shirin yanke hukunci tsakanin ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama da surukarsa kuma tsohuwar jakadiyar Najeriyaa, Lilian Onoh.

Rikicin ya faru a tsakaninsu ne bisa zargin da Lilian Onoh ta yiwa tsohon ministan a lokacin da yake ofis.

Kara karanta wannan

"A gwada matasa kawai": Tsohon shugaban kasa ya koka kan shugabancinsu

Zaman kotun Onyeama
Ana shirin yanke hukunci tsakanin tsohon minista da surukarsa. Hoto: Federal Ministry of Information and Culture, Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa rikicin da ya faru a tsakaninsu yana da nasaba da mutuwar aure da aka samu a baya tsakanin Onyeama da matarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi a zaman kotun

Tsohon ministan ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Zuba a Abuja ta tilasta Lilian Onoh ta biya shi N500m bisa zarginsa da cin hanci da ta yi.

Ya ce Lilian Onoh wacce ta kasance 'yar uwace ga tsohuwar matarsa ta zarge shi da cin hanci ne domin ta bata masa suna.

Onoh da tsohon minista a gaban kotu

A nata bangaren, Lilian Onoh ta bukaci kotun ta karba mata ₦2bn wajen tsohon minista, Geoffrey Onyeama.

Ta ce shigar da ita kara da Onyeama ya yi ya tayar mata da hankali sosai saboda haka ta bukaci a biya ta kudin a matsayin fansa.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Alkalin kotu ya dauki mataki

Bayan sauraron korafe-korafe daga dukkan bangarorin, alkalin kotun ya daga shari'ar, rahoton jaridar Leadership.

Ya ce a nan gaba kadan za a sanar da dukkan bangarorin ranar da kotun za ta dauka domin yanke hukuncin karshe kan shari'ar.

NLC ta shiga yajin aiki a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun shiga yajin aiki a Najeriya saboda kasa samun matsaya kan karancin albashi.

Yajin aikin na shirin jawo tsaida ayyuka a ma'aikatun gwamnati a faɗin Najeriya ciki har da makarantu, asibitoci, tashoshin jiragen sama da na ruwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng