Gaskiyar dalilin da yasa yan kasashen waje suke barin Najeriya kan Covid-19 - Onyeama
Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje, ya ce babu wani boyayyen manufa da ya sa wasu kasashe kwashe yan kasarsu daga Najeriya.
Akalla turawa 637 aka kwashe daga Najeriya da jumhuriyar Benin a ranar Alhamis.
Yunkurin ya sa mutane da dama tunanin ko akwai wani abun tashin hankali ne.
A lokacin lokacin taron manema labarai na kwanitin Shugaban kasa a kan COVID-19 a Abuja a ranar Juma’a, 3 ga watan Afrilu, wani dan jarida ya tambayi Onyeama ko barin kasar na da alaka da tsarin lafiyar Najeriya, inda ministan ya amsa da cewar ba haka bane.
Onyeama ya ce wadanda suka bar kasar sun yi hakan ne domin samun damar amfani da tsarin da suka saba, idan bukatar hakan ya taso.
Ya kara da cewa har yanzu ma’aikatan diflomasiyya na mafi akasarin kasashen na a kasar Najeriya sannan cewa basa tunanin barin kasar.
Jaridar The Punch dai ta ruwaito cewa wasu kasashen duniya da suka hada da Birtaniya, Amurka, Isra'ila da wasu kasashen da ke kungiyar tarayyar turai sun fara kwashe 'yan kasar su da ke Najeriya karkashin tsarin kar ta kwana da gwamnatin tarayya ta tanada.
KU KARANTA KUMA: Matar da ta kamu da Coronavirus ta arce daga wajen magani ta sha alwashin gogawa duk wanda yayi kokarin kama ta
A wani rahoton kuma mun ji cewa Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta umurci dukkan ofishin jakadancin ta a kasashen duniya su fara tattara sunayen 'yan Najeriya da ke son dawo wa gida kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Shugaban, Hukumar 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta ce an dauke wannan matakin ne sakamakon kiraye-kiraye da wasu 'yan Najeriya da ke kasanshen waje ke yi.
Sai dai ta bayyana cewa hukumar ta ce wadanda ke son dawowa gidan ne za su biya kudin jigilar dawo da su kuma za su mika kansu a killace su na tsawon makonni biyu idan sun dawo kasar.
Sanarwar da shugaban sashin hulda da al'umma na hukumar NIDCOM, Abdur-Rahman Balogun ya fitar ta ce duk wani dan Najeriya da ke son ya dawo gida ya tuntubi ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar da ya ke zaune.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng