“Ku Janye Wannan Yajin Aikin”: ’Yan Sandan Najeriya Sun Gargadi Ƙungiyoyin Ƙwadago
- Rundunar ‘yan sanda ta nemi 'yan kwadago da su koma teburin tattaunawa da kwamitin gwamnati kan sabon mafi ƙarancin albashi
- Rundunar ta NFF ta kuma gargadi kungiyoyin kwadago da su janye yajin aikin da suka fara yi domin kiyaye doka da oda a Najeriya
- A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, NFF ta ce ta hanyar tattaunawa ne kawai za a warware matsalar ba ta yajin aiki ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bukaci kungiyoyin kwadago da su janye yajin aikin da suka fara yi tare da komawa kan teburin tattaunawa da gwamnatin tarayya.
Rundunar ta ce ta hanyar tattaunawa, bangarorin biyu za su warware matsalar cikin ruwan sanyi domin yajin aikin na iya jefa ‘yan Najeriya a wahalhalu daban daban.
Rundunar ‘yan sandan ta mika wannan bukatar a wata sanarwa da kakakinta, Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune ta ruwaito sanarwar ta bayyana cewa kaucewa yajin aikin zai hana tabarbarewar doka da oda a kasar.
Sakon 'yan sanda ga 'yan kwadago
Sanarwar ta kara da cewa:
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya na kallon matakin 'yan kwadago na shiga yajin aiki a matsayin abin da zai iya haifar da tashin hankali da kuma rashin zaman lafiya a siyasance.
“Rundunar ta NPF a nan ta na bukatar ƙungiyoyin ƙwadago da su koma teburin tattaunawa da kwamitin gwamnati wanda ke da alhakin ƙayyade sabon mafi ƙarancin albashi."
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa da jama’a cewa an yi jibge jami'ai a duk fadin kasar domin tabbatar da cewa ‘yan kasar za su iya gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.
Majalisar dattawa ta aika sako ga Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta aika sako ga gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu kan yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka tsunduma a yau Litinin,
Majalisar ta nemi gwamnatin tarayyar da ta ci gaba da biyan kyautar karin albashi na N35,000 ga ma'aikatan kasar tunda kwamitin gwamnatin bai ba da rahoto ba.
Asali: Legit.ng