Gwamnatin Bola Tinubu Ta ci Bashin Naira Tiriliyan 20 a Shekarar Farko

Gwamnatin Bola Tinubu Ta ci Bashin Naira Tiriliyan 20 a Shekarar Farko

  • Cikin watanni 12 na fara mulkin Najeriya, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta aro N20.1trn daga hannun masu zuba hannun jari na cikin gida wanda ake ganin zai zama matsala
  • Rancen kudi na wannan shekara kari ne da kaso 117% na adadin da aka aro a bara, kuma masana na fargabar hakan zai kara ragargaza tattalin arziki
  • A ganin shugaban kungiyar cibiyar wayar da kan al’umma kan shugancin na gari da tabbatar da adalci, Kabiru Dakata, ka'idojin aro kudin matsala ce ga 'yan kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- A farkon shekarar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a yana jagorancin Najeriya, gwamnatin ta karbo aron N20.1trn daga hannun masu zuba jari na cikin gida.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi muguwar illar da bukatar NLC za ta yiwa ma'aikata

Wannan kari ne a kan kudin da kasar nan ta ranto a shekarar da ta gabata da kaso 117%, wanda hakan ya janyo damuwa kan halin da tattalin arzikin kasa zai shiga.

Bola Ahmed
Gwamnatin Bola Tinubu ta karbo bashin N20.1trn a cikin shekara guda Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamnati ta ci bashin N20tr a shekara

Vanguard News ta tattaro cewa masana sun fada damuwar yawan rancen zai iya karo hauhawar farashin kaya, karin kudin ruwa wajen biyan bashin da karuwar kudin rance daga masu kasuwanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma ana fargabar babban bankin kasa (CBN) zai iya kara kudin ruwa kan rancen da ake kara a bankuna.

Yadda gwamnatin Tinubu ta aro N20.1tr

An gano gwamnatin tarayya ta karbi basussukan ta hanyoyi da dama daga ‘yan kasuwa na cikin gida ta hanyar bayar da kadararta na bonds, da wasu kadarorin karkashin kulawar ofishin kula da basussuka (DMO).

Kara karanta wannan

An jero manyan nasarori 7 da Tinubu ya samu a kwana 365 da ya canji Buhari

Baya ga wadannan akwai wasu takardun asusun kasa da NTBs da babban bankin CBN ta bayar a madadin gwamnatin tarayya, kamar yadda Head Topics ta wallafa.

‘Gwamnati za ta illata tattalin arziki,’ masani

Masana tattalin arziki a Najeriya irinsu shugaban kungiyar cibiyar wayar da kan al’umma kan shugancin na gari da tabbatar da adalci, Kabiru Dakata na ganin karbar basussuka ba laifi ba ne idan za a yi amfani da su yadda ya dace.

Dakata ya ce kangin da ‘yan Najeriya ke ciki ya samo asali ne daga ka’idojin da masu bayar da bashin, irinsu IMF da bankin duniya ke gindayawa kasar.

Sannan ya ce sharudda irinsu cire tallafin man fetur, na wutar lantarki ko kara kudin ruwa su ne suka jefa kasar nan a kunci, wanda ya samo asali daga irin basussukan da ake karbowa.

‘Za a fita daga kangi,’ Shugaba Tinubu

A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnatin tarayya ta shaidawa ‘yan Najeriya cewa nan zuwa watan Disambar 2024 tattalin arziki zai fara farfadowa.

Kara karanta wannan

"Karancin kudi": Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki a jami'ar Kano, ta bayyana dalili

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka inda ya roki gwamnoni da sauran ‘yan Najeriya su bayar da hadin kai domin a kai ga nasara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel