Bayan Shekaru 13 Suna Jiran Tsammani, Gwamnati Ta Jiƙa Ƴan Fansho da Biliyoyi

Bayan Shekaru 13 Suna Jiran Tsammani, Gwamnati Ta Jiƙa Ƴan Fansho da Biliyoyi

  • Gwamnatin Zamfara ta biya yan fansho sama da 4,000 kudin da suka bi jihar bashi na tsawon shekara da shekaru
  • Wadanda aka biya kudin sun hada da tsofaffin malaman makaranta da ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar
  • Mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin yada labarai ya bayyana yadda aka raba kudin ka tsofaffin ma'aikatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara karkashin gwamna Dauda Lawal ta biya tsofaffin ma'aikatan jihar kudi sama da biliyan 5 da suka bi jihar bashi cikin shekaru.

Gwamnan Zamfara
Gwamnan Zamfara ya biya 'yan fansho bashin da suke bin jihar. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

An biya 'yan fansho kudinsu a Zamfara

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya ce tsofaffin ma'aikatan sun bi jihar bashin kudin ne har tsawon shekaru 13.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Sokoto ta rufe hotel da ake yada ayyukan barna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sulaiman Bala Idris ya nuna cewa an biya kudin ne bisa tsarin mataki bayan mataki da kuma tantancewa.

Adadin waɗanda suka samu kudin fansho

Gwamnatin ta bayyana cewa tsofaffin ma'aikatan ƙananan hukumomi da malaman makaranta 2,209 ne suka samu karbar kudin.

Sannan a bangaren tsofaffin ma'aikatan jihar Zamfara kuma an samu kimanin mutane sama da 1,642 da suka samu karbar kudin.

Kudin fanshon da aka biya ma'aikatan

Gwamnatin ta bayyana cewa tsofaffin ma'aikatan ƙananan hukumomi da malamai sun sama da Naira biliyan 2, sauran kudin kuma sun tafi ga tsofaffin ma'aiktan jiha.

Har ila yau gwamnatin ta tabbatar da cewa wadanda aka biya kudin suna rukunin tsofaffin ma'aikatan ne da suka yi ritaya daga shekarar 2012 zuwa 2019.

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ake zargin yana kai wa 'yan bindiga makamai a Plateau

Gwamnatin jihar ta ce biyan kudin yana cikin alkawuran da gwamnan jihar ya dauka na farantawa tsofaffin ma'aikatan Zamfara.

Gwamnati ta yi kira ga kungiyar ma'aikata

A wani rahoton, kun ji cewa, gwamnatin tarayya ta shirya dabarar hana kungiyar kwadago tafiya yajin aiki da take kokarin tsunduma.

Ministan yada labarai na kasa, Idris Muhammad ne ya yi kira ga kungiyar domin sake zama a teburin tattaunawa maimakon tafiya yajin aiki.

Hakan ya biyo bayan gaza samun daidaito tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya ne kan mafi karancin albashin ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel