Yajin Aiki Ya Tabbata: An Tashi Taron NLC da Majalisar Tarayya Ba Tare da Wata Nasara Ba
- Shugabannin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun ce babu ja da baya kan yajin aikin sai baba ta gani da za su shiga gobe Litinin
- Wannan na zuwa ne a yayin da aka tashi taron 'yan kwadagon da shugabannin majalisar dokokin kasar ba tare da wata nasara ba
- Amma shugabannin kwadagon sun yi alkawarin yin zama na musamman a tsakanin su domin duba bukatar majalisar dokin kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An tashi taron majalisar dokokin tarayya da kungiyoyin kwadago da aka yi a Abuja ba tare da an samu wata nasarar komai ba.
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun ce babu ja da baya kan yajin aikin da za su shiga gobe Litinin duk da kokarin majalisar dokokin na hana faruwar hakan.
Abin da kungiyoyin kwadago suka ce
Wakilan kungiyoyin kwadagon sun ce ba su da wani iko na hana tafiya yajin aikin har sai sun tuntubi 'yan kungiya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma shugabannin kwadagon sun yi alkawarin yin zama na musamman a tsakanin su domin duba bukatar majalisar dokin kasar.
Mun ruwaito cewa shugabannin majalisar dokokin kasar da shugabannin kwadago sun gana domin ganin yadda za a hana shiga yajin aikin.
Wadanda suka halarci taron sulhun
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyoyin kwadago sun fusata kan yadda gwamnati ta gaza karbar mafi ƙarancin albashi da suka gabatar mata.
Wadanda suka halarci taron sulhun sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume; shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila; ministan kudi, Dr Wale Edun; da ministan kasafi, Atiku Bagudu.
Sauran sun hada da karamin minista a ma’aikatar kwadago da samar da kayayyaki, Nkiruka Onyejiocha; Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris; Karamin ministan noma, Dr. Aliyu Sabi Abdullahi da sauran su.
Asali: Legit.ng