Sarautar Kano: Kungiya Ta Faɗi Dalilin Tube Aminu Ado da Mayar da Sanusi II da Abba Ya Yi
- Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta bankado cewa Gwamna Abba Kabir ya rushe masarautu ne domin kawar da hankulan mutane
- Kungiyar ta zargi gwamnan da neman rufa-rufa kan gazawarsa a matsayin gwamna tsawon shekara daya da ya yi a mulki
- Wannan na zuwa ne bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Kungiyar Arewa Truth and Justice Initiative ta yi martani kan rusa masarautun jihar Kano da Gwamna Abba Kabir ya yi.
Kungiyar ta caccaki Abba Kabir kan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II.
Kano: Kungiyar Arewa ta soki Abba Kabir
Kwadinetan kungiyar, Kwamred Momoh Idoko shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Legit ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Momoh ya ce Abba Kabir ya yi hakan ne domin yin rufa-rufa kan gazawarsa game da mulkin jihar da ya yi a cikin shekara daya.
Har ila yau, kungiyar ta caccaki gwamnan kan rushe-rushe da ya yi yayin da ya yi fatali wurin inganta ilimi da tsaro da tattalin arziki.
Kano: Kungiya ta zargi Abba da rufa-rufa
"A kokarinsa na kawar da hankalin mutane kan gazawar da ya yi a mulki, Gwamna Abba Kabir ya bijiro da maganar rushe masarautu a jihar."
"Mun yabawa mutanen Kano saboda kin bari a yi wasa da hankalinsu wurin kin amincewa da tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero."
- Momoh Idoko
Kungiyar ta kara da cewa daga cikin gwamnoni da suka cika shekara daya, Abba Kabir ne yafi kowa rashin tabuka wani abu a binciken da aka yi.
Kano: Sanusi II ya gargadi iyayen yara
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gargadi iyayaen yara wurin tarbiyantar da 'ya'yansu kan tafarki mai kyau.
Sarkin ya ce iyaye suna da muhimmiyar rawa da za su taka wurin tabbatar da tarbiyar 'ya'yansu a cikin al’umma.
Sanusi II ya ja kunnensu da su saka ido kan 'ya'yansu domin tabbatar da kare su daga miyagun kwayoyi da kuma halaye marasa kyau.
Asali: Legit.ng