Yajin Aiki: Akpabio da Abbas Sun Shiga Tattaunawar Gaggawa Da ’Yan Kwadago

Yajin Aiki: Akpabio da Abbas Sun Shiga Tattaunawar Gaggawa Da ’Yan Kwadago

  • An shiga wata ganawar gaggawa tsakanin shugabannin majalisar dokokin tarayya da kungiyar 'yan kwadago a Abuja
  • Majalisar dokokin kasar ta ce taron na da nufin "hana 'yan kwadago fara yajin aikin" da za su fara ranar Litinin, 3 ga Yuni, 2024
  • 'Yan kwadagon sun sha alwashin tsunduma yajin aikin saboda gaza samun matsaya da gwamnati kan mafi karancin albashi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugabannin majalisar dokokin tarayya sun saka labule da 'yan kwadago domin yin wani taron gaggawa a daren yau.

Wannan ganawar na daga wani yunkurin da 'yan majalisar ke yi na ganin 'yan kwadago ba su shiga yajin aikin da suka dauri aniyar farawa a gobe Litinin ba.

Kara karanta wannan

Abuja: Jerin ma'aikatu da hukomi 25 da kamfanin AEDC zai datse wa wutar lantarki

Majalisar tarayya ta shiga ganawa da 'yan kwadago
Akpabio da Abbas sun saka labule da shugabannin 'yan kwadago a Abuja. Hoto: @NLCHeadquarters, @NGRSenate
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da Festus Osifo na TUC ne suka wakilci 'yan kwadago a wannan taron, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ne suka wakilci bangaren majalisar majalisar dokokin tarayya.

Dalilin 'yan kwadago na fara yajin aiki

Majalisar dokokin kasar ta ce taron na da nufin "hana 'yan kwadago fara yajin aikin" da za su fara ranar Litinin, 3 ga Yuni, 2024, "wanda zai yi tasiri ga jama'a da tattalin arziki".

Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan rashin maslahar da aka samu tsakaninta da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.

Haka zalika, kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya da ta janye karin kudin wutar lantarki da ta yi a baya wanda har yanzu ba a janye ba.

Kara karanta wannan

Kano: "Zaman 'yan tauri a fadar Sarki Sanusi II ya jefa fargaba a zukatan jama'a" Dambazau

'Yan kwadago na neman karin albashi

A ranar Juma’a ne kungiyar kwadago ta ayyana shiga yajin aikin saboda kin amincewa da gwamnatin tarayya ta yi na kara karin mafi karancin albashin ma’aikata.

Jaridar The Punch ta ruwaito 'yan kwadagon sun ki amincewa da tayin gwamnati har sau uku kan karin mafi karancin albashin, na baya-bayan nan shi ne N60,000.

Daga baya TUC da NLC suka fice daga tattaunawar, inda suka dage a kan ₦497,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

Ana shan lita 1.6bn ta madara a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya na kwankwadar akalla lita biliyan 1.6 ta madara a duk shekara yayin da gwamnati ke kashe $1.5bn wajen shigo da ita.

Karamin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Abdullahi ya bayyana hakan a taron bikin ranar madara ta duniya ta 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel