Juyin Mulki: Janar Abdulsalami Ya Fallasa Wadanda Ke Ba da Kofar Kifar da Gwamnati

Juyin Mulki: Janar Abdulsalami Ya Fallasa Wadanda Ke Ba da Kofar Kifar da Gwamnati

  • Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana irin damar da ‘yan siyasa ke bayarwa a juyin mulki
  • Abdulsalami ya ce mafi yawan inda aka gudanar da juyin mulki, yawanci ‘yan siyasa ne ke ba da kofar faruwar hakan
  • Wannan martani na tsohon sojan na zuwa ne yayin da ake yawan samun juyin mulki musamman a kasashen Nahiyar Afrika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya magantu kan juyin mulki a gwamnati.

Abdulsalami ya ce babu yadda za a yi nasarar juyin mulki ba tare da hadin kan ‘yan siyasa ba a kowace kasa.

Kara karanta wannan

"A gwada matasa kawai": Tsohon shugaban kasa ya koka kan shugabancinsu

Janar Abdulsalami ya magantu kan juyin mulki a kasashe
Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar ya zargi 'yan siyasa da hannu a juyin mulki. Hoto: The Governor of Niger State.
Asali: Facebook

Juyin mulki: Abdulsalami ya zargi 'yan siyasa

Tsohon sojan ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar The Sun a jiya Asabar 1 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce duk inda aka samu juyin mulki tabbas akwai saka hannun ‘yan siyasa da suka ba soja damar hawa kujerar mulki.

“Duk abin da ya faru, akwai hannun ‘yan siyasa da ke ba da kofa domin soja ya hau kujerar mulki.”
“Idan ana gwamnati wanda babu adalci da daidaito, dole za a samu matsaloli wanda ka iya jefa kasa cikin matsala.”

- Abdulsalami Abubakar

Yawan juyin mulki da aka yi a Najeriya

Hakan ya biyo bayan yawan samun juyin mulki a wasu kasashen Afirka musamman Yammacin Nahiyar.

Tun bayan samun ‘yancin kan Najeriya a 1960, an yi juyin mulki akalla guda biyar a kasar kafin dawowa mulkin dimukradiyya a 1999.

Kara karanta wannan

Yayin da ake batun sauya tsarin mulki, Shettima ya fadi babban matsalar Najeriya

A yau dimukradiyya ta shika shekaru 25 kenan tun bayan dawo da ita a shekarar 1999 da Abdulsalami ya mika mulki ga Cif Olusegun Obasanjo.

Obasanjo ya bukaci ba matasa dama

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da mulki a Najeriya.

Obasanjo ya ce lokaci ya yi da ya kamata a ba sababbbin jini su gwada kwarewarsu wurin shugabancin kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da matasa ke neman ba su dama a kasar bayan dattawa sun shafe shekaru da dama suna mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel