Kogi: Gwamnati Ta Ceto Sauran Daliban Jami’a da Aka Sace Bayan Miyagu Sun Hallaka 2
- Gwamnatin jihar Kogi ta sanar da ceto dalibai takwas daga cikin 32 da aka sace a jihar a farkon watan Mayu da ta gabata
- Kwamishinan yada labarai a jihar, Kingsley Fanwo shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi 2 ga watan Yuni
- Kingsley ya ce a yanzu haka an kwato dalibai 30 kenan daga cikin wadanda aka sacen bayan hallaka biyu daga ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi – Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da ceto sauran daliban Jami’ar CUSTECH da aka sace a jihar.
Ceto daliban guda takwas da aka yi yanzu ya tabbatar da kwato mutane 30 kenan daga hannun ‘yan bindiga.
Gwamnatin Kogi ta ceto daliban Jami'a
Wannan na zuwa ne bayan sace dalibai guda 32 da maharan suka yi a farkon watan Mayu yayin da suka hallaka biyu daga ciki, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan yada labaran jihar, Kingsley Fanwo shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 2 ga watan Yuni, cewar Vanguard.
Kungsley ya ce gwamnan jihar, Usman Ododo ya ba da umarnin ba da duka gudunmawa domin hada daliban da iyayensu.
Gwamnan Kogi ya godewa Tinubu, jami'an tsaro
"Gwamnatin Kogi ta sanar da ceto dalibai takwas da aka sace a Jami'ar CUSTECH da ke Osara a jihar."
"Gwamntin jihar tana godiya ga Bola Tinubu wurin ba da gudunmawar samar da duka abin da ake bukata wurin ceto daliban."
"Haka kuma tana godewa Nuhu Ribadu da hafsan sojojin kasar da DSS da 'yan sanda da kuma 'yan tauri da suka taimaka kan lamarin."
- Kingsley Fanwo
Yan bindiga sun hallaka dalibai 2
A wani labarin, kun ji cewa Rundunar ƴan sanda a jihar Kogi ta sanar da mutuwar wasu daliban Jami'a da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta tabbatar da haka ne a yau Lahadi 26 ga watan Mayu ta bakin kwamishinan ƴan sanda, Bethrand Onuoha a birnin Lokaja.
Wannan na zuwa ne bayan sace dalibai akalla 32 da mahara suka yi a Jami'ar CUSTECH a jihar a farkon watan Mayu.
Asali: Legit.ng