'Yan Sanda Sun Cafke Magidanci Kan Siyar da Diyarsa a N1.5m

'Yan Sanda Sun Cafke Magidanci Kan Siyar da Diyarsa a N1.5m

  • Dubun wani magidanci mai ƙoƙarin siyar da ƴar cikinsa ta cika a jihar Bauchi bayan jami'an ƴan sanda sun yi caraf da shi
  • Magidancin mai suna Yusuf Umar wanda ma'aikaci ne ya yi yunƙurin siyar da ƴarsa mai shekara biyar a duniya kan kuɗi N1.5m
  • An cafke shi ne a cikin wani otel a garin Bauchi bayan wani jami'in ɗan sanda ya yi masa basaja a matsayin wanda zai sayi yarinyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi sun cafke wani magidanci bisa zarginsa da yunƙurin sayar da ɗiyarsa mai shekara biyar a duniya.

Magidancin dai ana zargin ya yi yunƙurin sayar da yarinyar ne kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi N1.5m.

Kara karanta wannan

Ana shirin shiga yajin aiki, kungiyoyin kwadago sun nemi sabuwar bukata wajen Tinubu

'Yan sanda sun cafke magidanci a Bauchi
'Yan sanda sun cafke magidanci kan yunkurin siyar da diyarsa a Bauchi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Wanda ake zargin mai suna Yusuf Umar mai shekara 49 a duniya ya yi iƙirarin cewa shi ma'aikaci ne a ƙaramar hukumar Warji ta jihar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ƴan sandan jihar Bauchi, Auwal Mohammed shi ne ya tabbatar da cafke wanda ake zargin a cikin wata sanarwa.

Yadda ƴan sanda suka cafke magidancin

A cewar rahoton ƴan sanda, Yusuf Umar ya shirya miƙa yarinyar hannun wani mutum, sai dai bai sani ba cewa mutumin mai shirin siyan yarinyar jami'in tsaro ne wanda ya yi basaja, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"A ranar 26 ga watan Mayun 2024, wanda ake zargin ya karɓo ɗiyarsa mai shekara biyar a duniya daga matarsa da suka rabu a ƙaramar hukumar Warji bisa cewa zai kaita wajen ƴar uwarsa da ke cikin garin Bauchi."

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

"Mahaifiyar ba ta da masaniya cewa ya riga da ya shirya miƙa yarinyar a hannun wani mutumi ba tare da sanin cewa jami'in ɗan sanda ba ne."

- Auwal Mohammed

Ya ƙara da cewa an cafke wanda ake zargin ne a cikin wani otel da ke cikin garin Bauchi.

Ƴan sanda sun hallaka shugaban ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa jami'anta sun yi nasarar daƙile harin garkuwa da mutane tare da ceto wanda aka yi yunkurin sacewa a Katsina.

Rundunar ta ce yayin artabu, dakarun ƴan sanda sun hallaka wani shugaban ƴan bindiga da ake kira, Auwalu Mahaukaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng