Gwamnati Ta Bijiro da Bukata Domin Hana Kungiyar Kwadago Tsunduma Yajin Aiki

Gwamnati Ta Bijiro da Bukata Domin Hana Kungiyar Kwadago Tsunduma Yajin Aiki

  • Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyar kwadago yayin da take shirin tsunduma yajin aiki a gobe Litinin, 3 ga watan Yuni
  • Ministan yada labara ne ya yi kiran a wani sako da wallafa inda ya koka kan kudin da kungiyar ke bukata a rika ba ma'aikata
  • Kungiyar kwadago ta yi kira ga gwamnatin tarayya ne kan biyan ma'aikata N494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Gwamantin tarayya ka kara mika kira na musamman ga kungiyar kwadago kan karin mafi ƙarancin albashi.

Ministan yada labarai na kasa, Muhammad Idris ne ya yi kira ga kungiyar a jiya Asabar, 1 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Tinubu ya bayyana dalilin kai gwamnonin jihohi 36 kotu

Gwadago
Gwamnati ta nemi zama da kungiyar kwadago kan karin albashi. Hoto: Federal Ministry of Information and Culture, Nigeria
Asali: Facebook

A sakon da ma'aikatar yada labarai ta kasa ta wallafa a shafin ta Facebook, ministan ya ce bukatar kungiyar kwadago ba abu bane zai za a iya dorewa a kan sa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin aiki: Gwamnati ta nemi sulhu, NLC

A yayin da kungiyar kwadago ta ayyana gobe Litinin, 3 ga watan Yuni a matsayin ranar fara yajin aiki, gwamnati ta yi kira kan dawowa teburin sulhu.

Ministan yada labarai na kasa, Idris Muhammad ne ya yi kiran a jiya Asabar inda ya bayyana cewa gwamnati ba za ta iya biyan kudin da kungiyar kwadago ke bukata ba.

Buƙatar NLC za ta ruguza tattali

Ministan yada labarai ya ce buƙatar kungiyar kwadago na biyan ma'aikata N494,000 zai sa gwamnati kashe N9.5tr duk shekara.

Ya ce hakan zai kai ga ruguza tattalin Najeriya inda zai jefa mutane sama da miliyan 200 cikin barazanar rasa aiki.

Kara karanta wannan

"Karancin kudi": Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki a jami'ar Kano, ta bayyana dalili

Har ila yau ministan ya ce ko da gwamnati ta iya karin kudin, ma'aikatu masu zaman kansu ba za su iya ba hakan kuma zai jefa ma'aikata cikin hadari.

Kokarin da gwamnatin Tinubu ta yi

Idris Muhammad ya kara da cewa maido da mafi ƙarancin albashi zuwa N60,000 na nufin gwamnati ta kara kaso 100% ga ma'aikata.

Ya ce saboda ƙoƙarin da gwamnatin ta yi ne ma'aikatu masu zaman kansu suka yarda da karin kudin.

Ya kuma tabbatar cewa karin kaso 1,547% da kungiyar kwadago ke bukata ba abu bane mai yiwuwa.

PDP ta magantu kan zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Umar Damagum ya bayar da tabbacin cewa jam'iyyar PDP na shirin dawowa kan turbar nasara a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Muƙaddashin shugaban PDP ya baiwa mambobin jam'iyyar hakuri kan rikicin cikin gida, inda ya ce za su karɓe mulki daga hannun APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel