Mafi Karancin Albashi: An Gano Dalilan Gwamnati 14 na Kin Sauya Matsayar N60,000

Mafi Karancin Albashi: An Gano Dalilan Gwamnati 14 na Kin Sauya Matsayar N60,000

Batun karancin albashi a Najeriya a Najeriya ya fada tsaka mai wuya bayan gwamnatin tarayya ta ki motsawa daga tayin ₦60,000 wanda kungiyoyin kwadago su ka ce ba zai sabu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Kungiyar kwadago ta NLC tafara shirin tsunduma yajin aikin gama-gari saboda kin amincewa da gwamnatin tarayya ta yi na biyan N497,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Wannan ya biyo bayan kafewa da gwamnatin ta yi kan cewa N60,000 za ta iya biyan ma'aikatan, kuma hakan ma bayan ta yi karin N3000 sau biyu ne.

Tinubu
Gwamnati ta bayyana dalilai 14 na kin tayin mafi karancin albashi 'mai kyau' Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/ Nigerian Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Yanzu dai gwamnati ta bayyana dalilai 14 da ta ce su ne ska hana ta yunkurin biyan mafi karancin albashi mai tsoka ga ma'aikatanta, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Kara karanta wannan

EFCC ta fara binciken Sanata Rabi'u Kwankwaso kan zambar kudin 'yan fansho

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashi: Dalilan gwamnati na kafewa su ne:

1. Biyan N35,000 ga dukkanin ma'aikatam da gwamnatin tarayya ke biya ta asusun bai daya

2. Ware N100bn na sayen motoci masu amfani da makamshin zamani na CNG da kayan sauya wasu ababen hawan zuwa wadanda ke amfani da CNG

3. Tallafin N125bn da gwamnati ta warewa masu kananan masana'antu

4. Rabon tallafin N25,000 ga gidaje miliyan 15 na tsawon watanni uku

5. Aron N185bn ga jihohi domin su rage radadin cire tallafin man fetur ga al'umarsu

6. Ware N200 domin nome kadada masu tarin yawa domin bunkasa samar da abinci a Najeriya

7. Ware N75bn domin karfafa bangaren masana'antun kasar

8. Ware makudan kudi har N1trn domin bayar da lamunin karatu ga daliban manyan makarantu

9. Fito da abinci tan 42,000 daga rumbunan abinci mallakin gwamnati ga 'yan kasa

Kara karanta wannan

Tinubu ya samu sauƙi a bukatar da ƴan ƙwadago suka gabatar kan mafi ƙarancin albashi

10. Saye tare da raba shinkafa tan 60,000 daga masu sarrafa shinkafa domin rabawa talakawan Najeriya

11. Karin kaso 25% da 35% na albashin wasu daga ma'aikatan kasar nan

12. Tallafin kaso 90% kan harkar lafiya ga ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka yi rajista da tsarin taimakekeniyar lafiya na NHIS

13. Kaddamar da aikin layin dogo a babban birnin tarayya Abuja domin rage wahalar sufuri a birnin har zuwa karshen shekara

14.Amincewar gwamnati na bawa ma'aikatanta damar neman hanyar samun kudin shiga, inda ta amince da bijiro musu da wasu ayyukan fasahar zamani

TUC ta yi martani kan batun albashi

A karin bayanin da ya yiwa Legit Hausa, tsohon shugaban kungyiyar 'yan kwasuwa ta kasa (TUC) na reshen jihar Kano, ya bayyana cewa wakilan gwamnati ba su zauna da su a zaman karshe ba.

A cewarsa karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce kadai ta halarci zaman.

Kara karanta wannan

Karin albashi: An sanya ranar sake hawa teburin tattaunawa tsakanin nlc da gwamnati

Sani Babangida ya ce babu dalilin da za a ninka kudin wuta da farashin man fetur kusan sau uku, amma a gaza ninka albashin ma'aikata na wannan adadi yadda za su iya daukar dawainiyarsu ba.

Ya ce suna nan kan bakar su na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani domin biwa ma'aikatan Najeriya hakkokinsu.

Albashi: NLC ta yi watsi da tayin gwamnati

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyoyin kwadago na NLC da ta ta 'yan kasuwa TUC sun yi watsi da sabon tayin mafi karancin albashi da gwamnati ta yi musu.

Sun nemi gwamnatin tarayya ta biya N494,000, ragin N3000 daga 497,000 da suka bukaci gwamnatin ta bayar bayan ta yi musu tayin N60,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.