Matawalle Ya Dauki Zafi Kan Kisan Sojoji a Abia, Ya Fadi Matakin Dauka
- Ƙaramin ministan tsaro na Najeriya, ya yi Allah wadai da kisan gillar da ƴan ta'adda suka yiwa sojoji a jihar Abia
- Bello Matawalle ya bayyana kisan a matsayin rashin imani inda ya sha alwshin cewa za a cafko masu hannu a ciki domin su fuskanci hukunci
- Ministan ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan sojojin da rundunar sojojin Najeriya bisa wannan gagarumin rashin da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi magana kan kisan da aka yi wa sojoji a jihar Abia.
Ƙaramin ministan ya bayyana cewa za a cafke masu hannu a wannan mummunan ɗanyen aikin.
An hallaka sojojin ne dai yayin da suke bakin aiki a wani shingen bincike a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar sojoji ta sha alwashin ɗaukar fansa kan kisan yayin da gwamnatin jihar Abia ta sanya ladan Naira miliyan 25 domin gano waɗanda suka yi kisan.
Me Matawalle ya ce kan kisan sojojin?
Da yake martani a ranar Asabar, Matawalle ya bayyana harin a matsayin rashin imani da tsabar mugunta, cewar rahoton jaridar TheCable.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar, Henshaw Ogubike, ya fitar, rahoton Westernpost ya tabbatar.
"Mummunan kisan gillar da aka yi wa sojoji a jihar Abia an yi shi ne ba tare da wata takala ba yayin da suke bakin aiki na kare ƴan ƙasa daga barazanar ƴan ta'adda."
"Matawalle yana miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan sojojin da rundunar sojojin Najeriya, sannan ya buƙaci sojoji da kada harin ya sare musu gwiwa."
"Ya sake jaddada jajircewar gwamnati wajen goyon bayan sojoji a ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen IPOB, ESN da sauran masu laifi a sauran yankunan ƙasar nan domin tabbatar da tsaro a ƙasa."
- Henshaw Ogubike
Ƴan IPOB sun farmaki sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta yi gagarumar asara bayan mambobin haramtacciyar ƙungiyar nan ta IPOB dake rajin kafa ƙasar Biafra ta kai musu hari.
Ƴan ta'addan su kimanin mutum 15 dake cikin wasu motoci sun kashe sojoji guda huɗu, tare da ƙona ababen hawa da dama a harin.
Asali: Legit.ng