Mufti Yaks: Fitaccen Matashi Mai Wa'azin Musulunci Ya Rasu, Mufti Menk Ya Yi Alhini

Mufti Yaks: Fitaccen Matashi Mai Wa'azin Musulunci Ya Rasu, Mufti Menk Ya Yi Alhini

  • Allah ya karbi rayuwar matashi mai wa'azin addinin Musulunci, Abdullateef Aliyu Maitaki a yau Asabar a birnin Minna da ke jihar Niger
  • Matashin da aka fi sani da Mufti Yaks ya kasance yana fadakar da mutane kan bin tafarkin addinin Musulunci sau da kafa
  • Fitaccen Malamin Musulunci, Mufti Menk wanda matashin ke kwaikwayo shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Matashin mai da'awar Musulunci, Abdullateef Aliyu Maitaki ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin wanda aka fi sani da Mufti Yaks ya kasance yana kwaikwayon fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Isma'il Ibn Menk (Mufti Menk).

Kara karanta wannan

Kano: Jawabin karshe da Sanusi II ya yi kafin maida shi gadon sarautar Dabo

An shiga jimami bayan rasuwar matashi mai wa'azin Musulunci, Mufti Yaks
Fitaccen matashi mai da'awar Musulunci, Mufti Yaks ya kwanta dama. Hoto: Mufti Yaks.
Asali: Facebook

Mufti Menk ya yi alhinin rasuwar Yaks

Fitaccen Malamin addini, Sheikh Isma'il Ibn Menk shi ya sanar da rasuwar matashin a shafinsa na X a yau Asabar 1 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mufti Menk ya ce ya kadu da samun labarin rasuwar matashin inda ya yi addu'ar ubangji ya yi masa rahama.

"Na kadu da samun labarin rasuwar matashi Abdullateef Maitaki da safiyar yau, matashi ne mai kwarewa kuma da ke kokarin yada abubuwan alheri."
"Ina rokonka Allah ya yi masa rahama ya karbi ayyukansa masu kyau da kuma saka masa da aljanna firdausi, Ameen."

- Mufti Menk

Gudunmawar da Mufti Yaks ya ba Musulunci

Matashin ya sadaukar da rayuwarsa wurin koyar da addini da kuma wa'azi domin fadakar da al'umma.

Rahotanni sun sanar da cewa tuni aka yi sallar jana'izar matashin a yau Asabar da misalin karfe 10:00 na safe a birnin Minna da ke jihar Niger.

Kara karanta wannan

Bidiyon dubban mutane da suka tari Sarkin Kano bayan Juma'a, ya aika sako a huduba

Tsohon shugaban EFCC ya kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa Tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 61.

Marigayin ya rasu ne a kasar Masar yayin da ya je domin yin jinya kamar yadda aka sanar da safiyar yau Lahadi 26 ga watan Mayu.

Kafin rasuwarsa, Lamorde ya rike shugabancin hukumar a mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.