Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ke Dagula Arewa
- Yayin da ake ci gaba da samun matsaloli a yankin Arewacin Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi karin haske kan musabbabinsu
- Kwankwaso ya daura alhakin wadannan matsalolin kan rashin adalci da kuma rashin kwarewa na shugabanci a kasar
- Sanatan ya bayyana takaici yadda ake yaudarar mutane da kudi da taliya da kuma atamfa domin zaben azzaluman shugabanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sanata Rabiu Kwankwaso ya magantu kan tabarbarewar lamura a yankin Arewacin Najeriya.
Kwankwaso ya bayyana rashin iya shugabanci da rashin adalci a matsayin manyan abubuwa da ke lalata lamura a yankin.
Kwankwaso ya yi korafi kan yaudara a zabe
Sanatan ya bayyana haka ne yayin hira da BBC Hausa bayan cikan dimukradiyya shekaru 25 a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Kano har ila yau, ya koka kan yadda ake yaudarar mutane da taliya wurin zaben rubabbun shugabanni.
"Dimukradiyya abu ne mai kyau tun da ta fi mulkin soja, sai dai akwai matsaloli da ke tattare da tsarin wanda ba haka ya ke ba."
"Mafi yawan mutane saboda talauci ana amfani da su wurin ba su magi da taliya da atamfa domin su zabi wadanda za su ci gaba da musu azaba."
"A fahimta ta duk wasu matsalolin Arewa rashin iya shugabanci ne da kuma rashin adalci."
"Rashin adalci ya ke sa kaga mutane suna kukan kura suna yin wadansu abubuwa domin su taimakawa kansu."
- Rabi'u Kwankwaso
Kwankwaso ya magantu kan siyasar uban gida
Kwankwaso ya yi magana kan zargin kaka-gida a mulkin Abba kabir inda ya ce wannan shugabanci ake ki kira ba kaka-gida ba wanda kuma duk duniya akwai haka.
EFCC ta gayyaci Kwankwaso kan badakala
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar hana yiwa tattalin arzikin na kasa ta’annati (EFCC) ta mika goron gayyata ga jagoran NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hukumar ta bude binciken tsohon gwamnan na Kano da zambar kudin fansho da yawan su ya kai N2.5bn.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni hukumar ta gayyato tsohon gwamnan Kano tare da yi masa wasu tambayoyi.
Asali: Legit.ng