Kotu Ta Dauki Mataki Kan Abba Kyari Bayan Watanni 27 a Gidan Kaso, Akwai Sharuɗa

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Abba Kyari Bayan Watanni 27 a Gidan Kaso, Akwai Sharuɗa

  • A karshe, an sake tsohon dan sanda, DCP Abba Kyari daga gidan gyaran hali bayan shafe watanni 27 a kulle a birnin Abuja
  • An sake Kyari ne bayan ya cika duka ka'idojin ba da beli da ake bukata daga gare shi kamar yadda hukumomi suka tabbatar
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar gidan gyaran hali na Kuje, Adamu Duza ya fitar a jiya Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Bayan shafe watanni 27 a kulle, tsohon dan sanda, DCP Abba Kyari ya shaki iskar ƴanci.

Kyari ya shafe shekaru biyu a kulle a gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Abuja tun bayan cafke shi a 2022.

Kara karanta wannan

Shekara 1 a ofis: Jerin ministoci 10 da suka fi kowa kokari a gwamnatin Tinubu

Kotu ta ba da belin Abba Kyari bisa wasu sharuɗa
Kotu ta ba da belin Abba Kyari bayan shafe shekaru 2 a gidan kaso. Hoto: Abba Kyari, Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Musabbabin sakin Abba Kyari daga gidan kaso

An sake Kyari ne bayan ya cika ka'idojin beli wanda ya hada da ajiye fasfo dinsa a kotu da halartar ofishin NDLEA yayin belin nasa, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin gidan gyaran hali na Kuje, Adamu Duza shi ya tabbatar da haka a jiya Juma'a 31 ga watan Mayu.

Duza ya ce an sake Kyari bayan cika ka'idojin karbar beli a jiya Juma'a 31 ga watan Mayu bayan shafe watanni a kulle, cewar Daily Post.

"Kyari ya cika duka ka'idojin ba da beli kuma an sake shi a yau Juma'a."

- Adamu Duza

An cafke Kyari ne a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kan zargin ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Hukumar NDLEA ta cafke Kyari ne da wasu mutane guda hudu da suka haɗa da Sunday Ubia da Bawa James da Simon Agirigba da kuma John Nuhu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi awon gaba da fitaccen malamin addinin Musulunci da matarsa a Abuja

An ba Abba Kyari belin makwanni 2

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon dan sanda, DCP Abba Kyari belin makwanni biyu.

An ba Abba Kyari belin ne yayin da ya ke cikin jimamin mutuwar mahaifiyarsa da ta rasu a farkon watan Mayu da muke ciki.

Wannan mataki na kotun na zuwa ne bayan Kyari ya shafe watanni 27 a kulle kan zargin ta'ammali da safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel