Yadda Basarake Ya Karbi Cin Hanci a Hannun 'Yan Bindiga Domin Su Hallaka Mutane a Kauyensa
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta daɗe tana addabar jihar
- Dikko Radda ya bayyana cewa an cafke wani basarake da ya ƙarbi cin hanci a hannun ƴan bindiga domin su shiga ƙauyensa su kashe mutane
- Ya bayyana cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin shawo kan matsalar talauci wanda shi ne ke rura wutar matsalar rashin tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya bayyana yadda wani basarake ya ƙarbi cin hanci a hannun ƴan bindiga domin su ci karensu babu babbaka a ƙauyensa.
Gwamnan ya bayyana cewa basaraken wanda ke da sarautar Magajin Gari ya ƙarɓi N700,000 a hannun ƴan bindigan, inda suka shigo ƙauyen suka hallaka mutum 30.
Menene ke rura rashin tsaro a Katsina?
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin shawo kan matsalar talauci saboda ta fahimci yadda yake rura wutar tsarin tsaro.
A cewarsa abin takaici ne saboda N2,000 wasu mutane za su bayar da bayanai ga ƴan bindiga kan makwabtansu ko ƴan uwansu.
Wane basarake aka cafke?
Dangane da basaraken da aka samu da laifin haɗa baki da ƴan bindiga, gwamnan ya tabbatar da cewa ya ƙarbi N700,000 a hannunsu domin su shiga ƙauyensa.
"Eh mun cafke wani Magajin Gari a ƙauyen Guga cikin ƙaramar hukumar Bakori saboda haɗa baki da ƴan bindiga."
"An ba shi N700,000 domin ya bari ƴan bindiga su shiga ƙauyensa inda suka kashe fiye da mutum 30."
- Dikko Umaru Radda
Wace nasara aka samu kan ƴan bindiga?
Dangane da ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi domin magance rashin tsaro a jihar, Gwamna Radda ya ce rundunar tsaro ta haɗin gwiwa a jihar ta kashe ƴan bindiga 35 a shekarar da ta gabata.
Hakazalika, an cafke ƴan bindiga 363 inda aka miƙa su wajen ɓangaren shari'a yayin da aka ceto mutum 565 da aka yi garkuwa da su.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wata mazauniyar ƙauyen Guga, mai suna Sadiya wacce ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a wajen watan Disamban 2023.
Ta bayyana cewa sharri aka yiwa Magajin Garin kuma daga baya an gano gaskiya inda yanzu haka yake kan kujerarsa.
Ƴan bindiga sun hallaka mutum 17
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kao hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun hallaka mutum 17 a harin ta'addancin da suka kai kan bayin Allah yayin da suka yi awon gaba da wasu mutum biyu zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng