Gwamna Ya Sa Tukuicin N25m Ga Duk Wanda Ya Taimaka Aka Kama Waɗanda Suka Kashe Sojoji
- Gwamnatin Abia karkashin jagorancin Gwamna Alex Otti ta yi tir da harin ƴan bindiga wanda ya yi ajalin sojoji a Aba
- Kwamishinan yada labarai na jihar, Prince Okey Kanu, ya ce kisan da aka yi wa sojojin babban cin fuska ne ga kudurin kawar da masu aikata laifuka a jihar
- Kanu ya ce gwamnatin Gwamna Alex Otti ta sanya ladar Naira miliyan 25 ga duk wanda ya taimaka aka cafke wadanda suka kashe sojoji biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya sanya tukuicin Naira miliyan 25 kan wadanda suka kashe sojojin Najeriya biyar a mahadar Obikabia, tsaunin Ogbor a Aba.
Gwamnan ya yi alƙawrin cewa duk wanda ya taimaka da sahihan bayanai har aka cafke makasan za a ba shi waɗannan kuɗaɗe N25m a matsayin lada.
Idan baku manta ba wasu ƴan bindiga da ke ƙoƙarin ƙaƙaba dokar zaman gida bisa umarnin ƙungiyar ƴan aware IPOB sun ƙona motocin jami'an tsaro biyu a harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Otti ya sa tukuicin N25m
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Abia, Prince Okey Kanu ne ya bayyana ladan da za a ba duk wanda ya kawo bayanai, a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a
A rahoton Vanguard, Kanu ya ce gwamnatin Abia ta yi Alla-wadai da farmakin kana ta miƙa sakon ta'aziyya ga hafsan rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja.
"Gwamnatin Abia za ta bayar da tukuicin N25m ga duk wanda ya kawo sahihan bayanai da za su taimaka a cafke ko da mutum ɗaya ne mai hannu a wannan harin."
Kwamishinan ya bayyana harin da aka kaiwa sojojin a matsayin wani koma baya da cikas a ƙoƙarinsu na kakkabe duk wani mai aikata miyagun laifuka a faɗin jihar.
Kanu ya ce harin babban koma baya ne ga kokarin magance ayyukan ta'addanci, wanda ke neman mayar da Abia cikin rami da rashin tsaro, in ji Premium Times.
Ƴan sanda sun shiga ruɗani a Kano
A wani rahoton kuma ƴan sanda sun rasa umarnin da za su ɗauka yayin da kotuna biyar suka bayar da umarni masu cin karo da juna kan rikicin sarautar Kano.
Kwamishinnan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya ce sun miƙa umarnin kotunan ga sufetan ƴan sanda na ƙasa, shi ma ya tuntuɓi ministan Tinubu.
Asali: Legit.ng