An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyukan Jihar Katsina

An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyukan Jihar Katsina

  • Ƴan bindiga sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kankara da ke jihar Katsina inda suka hallaka mutane masu yawa
  • Miyaggun ƴan bindigan sun hallaka mutum 17 a hare-haren da suka kai a ƙaramar hukumar yayin da suka sace mutum biyu
  • Daga cikin mutanen da suka hallaka har da manoma yayin da suka sha alwashin hana su noma gonakinsu a wannan daminar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun hallaka aƙalla mutum 17 a wasu hare-hare da suka kai a wasu ƙauyukan jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a ƙaramar hukumar Kankara ta jhar Katsina.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun hallaka mutum 17 a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Katsina

Harin baya-bayan nan ya auku ne a ranar Alhamis, lokacin da ƴan bindigan suka farmaki wata motar haya a kusa da Dan Marke a kan hanyar Kankara zuwa Marabar Kankara lokacin da take dawowa daga kasuwa.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki sojoji a shingen bincike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa an hallaka mutum biyar a wajen ciki har da direban motar mai suna Dan Mashi.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da suka samu raunuka an kai su asibiti inda ake duba lafiyarsu.

Ya ƙara da cewa an sace biyu daga cikin fasinjojin motar ciki har da ɗan direban motar da aka hallaka.

Hakazalika a safiyar ranar Alhamis, an hallaka manoma bakwai a gonakinsu a ƙauyen Katsalle kusa da Mabai cikin ƙaramar hukumar Kankara.

Wani mazaunin yankin wanda ya tabbatar da lamarin ya ce a farkon makon nan ƴan bindiga sun hallaka mutum uku a gonakinsu yayin da suka sha alwashin cewa ba za su bari manoma su yi noma ba a wannan daminar.

Haka kuma ƴan bindiga sun hallaka wasu mutum biyu a Unguwar Daudun Noma bayan sun farmaki motar da suke ciki.

Kara karanta wannan

"Mun gaji da rikici": Matasa sun ɗauki zafi, sun shiga fada sun taso sarki waje

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq domin samun ƙarin bayani kan hare-haren.

Sai dai, kakakin rundunar ƴan sandan bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba sannan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba.

Ƴan bindiga sun farmaki ƴan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki tawagar mambobi biyar na majalisar dokokin jihar Benuwai a kan titin Makurɗi zuwa Gboko.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kai wa ƴan majalisar hari da misalin ƙarfe 10:00 na dare a daidai ƙauyen Tyomu mai nisan kilomita 16 zuwa Makurɗi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng