Kano: Yadda Sarki Sanusi II da Aminu Ado Bayero Suka Yi Sallar Jumu'a a Masallatai 2
- Hankali ya kwanta yayin da Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero suka yi Jumu'a a masallatai daban-daban a Kano
- Sarki Sanusi II ya jagoranci sallah a babban masallacin Ƙofar Kudu yayin da Aminu Bayero ya yi Jumu'a a ƙaramar fadar Nasarawa
- Tun farko dai rundunar ƴan sanda ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa dukkan sarakunan zasu yi Jumu'a a masallacin Ƙofar Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero sun yi sallar Jumu'a a wurare daban-daban yau 31 ga watan Mayu, 2024.
Sanusi II ya jagoranci magoya bayansa a babban masallacin fadar Ƙofar Kudu, inda ya yi limancin sallar Jumu'a.
Sanusi II da Aminu sun yi Juma'a
A ɗaya ɓangaren kuma sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi Jumu'a tare da magoya bayansa a gidan sarki da ke Nasarawa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun farko dai magoya bayan sarakunan sun fara yaɗa jita-jitar cewa Sanusi II da Aminu sun shirya gudanar da sallar Jumu'a a babban masallacin fadar sarki.
Wannan lamari dai ya jefa tsoro da fargaba a zuƙatan mazauna Kano saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo idan sarakunan suka haɗu a wuri ɗaya.
Hankula sun kwanta a garin Kano
Sai dai kuma daga baya, sarakunan sun nuna cewa kowanen su zai yi sallah a masallaci daban, lamarin da ya sa aka samu kwanciyar hankali a tsakanin Kanawa.
Daga ƙarshe dai Sarki Sanusi II ya yi limancin Jumu'a a babban masallacin Ƙofar Kudu yayin da Aminu Bayero ya yi sallah a ƙaramar fadar Nasarawa.
Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Gumel, ya karyata rade-radin da ake yaɗawa na cewa Aminu Bayero zai yi sallar Juma’a a fadar da Sanusi ke ciki.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna ya fitar, CP Gumel ya bayyana rade-radin a matsayin karya, Tribune Nigeria ta ruwaito.
“Rundunar ‘yan sanda na kira ga jama’a da su yi watsi da labaran karya da ake yadawa a soshiyal midiya cewa Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Juma’a a babban masallacin Kofar Kudu."
Gwamnan Kano ya gana da Nuhu Ribaɗu
A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Nuhu Ribado yayin da ake ci gaba da dambarwar masarautar Kano.
Darakta janar ga gwamna Abba kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka jibanci ci gaban kasa da jiha.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng