Bidiyon Dubban Mutane da Suka Tari Sarkin Kano Bayan Juma'a, Ya Aika Sako a Huduba

Bidiyon Dubban Mutane da Suka Tari Sarkin Kano Bayan Juma'a, Ya Aika Sako a Huduba

  • Dubban mutane ne suka tarbi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yayin da yake dawowa daga sallar Juma'a a yau
  • Matasa da yara da kuma mata ne suka yi dandazo domin nuna goyon baya ga sabon Sarkin bayan kammala sallar Juma'a
  • Hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren yada labarai, Hassan Sani Tukur shi ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa na X

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin Kano.

Yayin da yake dawowa daga masallacin, dubban mutane ne suka tarbe shi domin nuna goyon baya gare shi.

Sanusi II ya tura muhimmin sako a huduba, dubban jama'a sun tarbe shi
Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Juma'a a yau. Hoto: @Naija_PR, @HrhBayero.
Asali: Twitter

Kano: Yadda aka tari Sarki Sanusi II

Kara karanta wannan

Kano: Tashin hankali yayin da Sarki Sanusi II da Aminu Ado ke shirin sallar Jumu'a

Hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren yada labarai, Hassan Sani Tukur ya wallafa bidiyon dandazon jama'a da suka tarbi Sarkin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, an gano dubban mutane suna murna da kuma nuna tsantsan goyon bayan ga sabon Sarkin.

Kano: Sakon Sanusi II yayin hudubar sallah

Yayin huduba lokacin sallar Juma'a, Sarki Sanusi II ya ce duk wanda ya yi imani da ƙaddarar ubangji ba zai taba kin sallamawa wani hukunci da Allah ya yi ba.

"Duk wanda ya yi imani Allah ne kadai ke bayarwa, dole zai yi imani da duk wani hukunci na Ubangiji, babu wanda zai tuhume shi hujja kan wani abu."

- Muhammadu Sanusi II

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigima kan sarautar jihar Kano tun bayan tube sarki na 15, Aminu Ado Bayero a makon jiya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi nadin farko

Masanin doka ya magantu kan sarautar Kano

Kun ji cewa wani kwararren mai shiga tsakani kuma masanin doka, Umar Sa'ad Hassan ya ce har yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano a doka.

Umar ya bayyana cewa sarki na 15, Alhaji Amunu Ado Bayero ne halastaccen sarkin Kano ba Muhammadu Sanusi II ba.

Ya yi bayanin cewa Babbar Kotun Tarayya mai zama a Kano ta bayar da umarnin a dakatar da sabuwar dokar masarauta wadda majalisar dokokin jihar ta yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel