An Tsokano Rigima: Sojoji Sun Rantse Sai Sun Murƙushe 'Yan IPOB Bayan Kisan Jami’ai
- Rundunar sojin Najeriya ta yi alwashin murƙushe kungiyar yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB)
- Lamarin ya biyo bayan kashe sojojin Najeriya biyar da yan ta'addan suka yi saboda dokarsu ta tursasa zaman gida
- Kungiyar gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya ta yi magana kan kisan gillar da 'yan kungiyar suka yi wa sojojin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Abia - Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin murƙushe kungiyar yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB).
'Yan IPOB sun tabo tsuliyar dodo
Hakan ya biyo bayan wani hari da yan ta'addan suka kai ga sojin Najeriya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji kimanin biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun yi kone-kone a lokacin da suka kai hari ga sojojin.
Sojoji za su dauki fansa kan IPOB
A yau Juma'a jami'in yada labaran rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya shaida cewa rundunar za ta dauki mataki a kan yan ta'addan.
Manjo Janar Edward Buba ya ce a wannan karon rundunar sojin za ta tabbatar da murƙushe yan ta'addan baki daya.
Ya kuma yi kira na musamman ga al'ummar yankin da su ba rundunar sojin hadin kai yadda ya kamata domin ƙarar da yan ta'addan baki daya.
A ina 'yan IPOB suka kashe sojojin?
Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da cewa an tura sojojin ne aiki a yankin karamar hukumar Obingwa a jihar Abia.
Ya ce an tura sojojin ne domin aikin wanzar da zaman lafiya a wasu wurare amma sai yan ta'addan suka yi kwanton bauna suka far musu.
Jami'in yake cewa harin ya jawo kashe jami'an soji biyar wanda ya sa rundunar sojin kasar cikin jimami duk da cewa suna shirin daukar fansa kuma gwamnonin yankin sun yi Allah wadai da aikin.
Mahaifi ya daki malama a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa wani mahaifi mai suna Muhammad Jimeta ya shiga har makarantar da yar sa take karatu ya lakaɗawa malama duka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa malamar mai suna Sekinat Adedeji tana dauke da jariri mai wata uku da haihuwa mutumin ya afka mata da duka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng