Benue: Ƴan bindiga da dama Sun Bakunci Lahira Yayin da Sojoji Suka Far Masu a Arewa

Benue: Ƴan bindiga da dama Sun Bakunci Lahira Yayin da Sojoji Suka Far Masu a Arewa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun ragargaji ƴan bindiga a samame daban-daban da suka kai maɓoyarsu a jihar Benuwai
  • A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce sojojin sun kashe ƴan ta'adda uku kuma sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su
  • Jami'an sojojin sun kwato makamai da kayan aiki kamar babura da bindigu ƙirar AK47 daga hannun ƴan bindigar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda uku a kauyen Sankara da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benuwai.

Haka nan kuma dakarun sojojin sun kubutar da mutum biyu da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su a samamen da suka kai a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

ISWAP ta ba mazauna garin Kukawa zabin barin gidajensu ko a kashe su

Sojojin Najeriya.
Dakarun sojoji sun samu nasara kan ƴan ta'adda a jihar Benuwai Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Sojoji sun kubutar da mutane a Benue

Rundunar sojojin kasa ta Najeriya ce ta bayyana wannan nasara a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"A bisa bayanan sirrin da aka samu, sojoji sun kai farmaki kan maboyar masu garkuwa a Sankara, karamar hukumar Ukum, inda suka kashe 'yan ta'adda uku tare da kubutar da wasu mutane biyu."

Dakarun sun kuma samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, bindigu na gida, wayoyin hannu iri-iri, kakin jami'an tsaro, da babur guda daya.

An ceto soja daga hannun masu garkuwa

A wani samame makamancin haka, sojojin sun ceto wani abokin aikinsu soja da aka yi garkuwa da shi a yankin Goh da ke karamar hukumar Gwer ta yamma a Benuwai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kai farmaki kan 'yan ta'adda a Benue, sun ceto wasu jami'an soji da aka sace

Duk da babu cikakken bayani game da sojan da aka ceto, rundunar ta ce an yi garkuwa da shi ne a ranar 25 ga watan Mayu kuma yanzu haka ana duba lafiyarsa a asibiti.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Haka zalika, a ranar 30 ga Mayu, 2024, an ceto Laftanar Bot Elisha da wasu fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su yayin da suke tafiya a cikin motar Peace Mass Transit Bus daga Abuja zuwa Fatakwal.

Ƴan bindiga sun sace ɗaliban jami'a

A wani rahoton kun ji cewa wasu mahara sun tare daliban jami'a mata, sun yi awon gaba da su a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ranar Asabar.

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa an sace ɗalibai mata biyu na jami'ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi (JOSTUM) kwanan nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel