Ana Cikin Rigimar Sarautar Kano, Ganduje Ya Sake Roƙon Ƴan Najeriya

Ana Cikin Rigimar Sarautar Kano, Ganduje Ya Sake Roƙon Ƴan Najeriya

  • Yayin da ake tsaka da rikicin masarautun Kano, shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya roki ƴan Najeriya kan mulkin Bola Tinubu
  • Ganduje ya ce tun yanzu tsare-tsaren da Tinubu ke dauka sun fara haifar da ɗa mai ido a cikin shekara daya da ya yi kan mulki
  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana haka ne yayin kaddamar da littafin cika Tinubu kwanaki 365 a kan mulkin Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya ce Shugaba Bola Tinubu ya shirya kawo sauyi a kasar.

Abdullahi Ganduje ya ce tsare-tsaren da Bola Tinubu yake dauka a kasar sun fara haifar da ɗan mai ido tun ba a je ko ina ba.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, jam'iyyar Kwankwaso ta aike da saƙo ga Bola Tinubu

Ganduje ya roki ƴan Najeriya ana tsaka dambarwar sarautar Kano
Duk da rikicin sarautar Kano, Ganduje ya sake rokon ƴan Najeriya kan mulkin Tinubu. Hoto: @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

Tinubu: Ganduje ya bukaci karin haƙuri

Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne yayin taron kaddamar da littafi game da kwanaki 365 na Tinubu a Najeriya a birnin Tarayya Abuja, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya bukaci ƴan Najeriya da su kara hakuri a mukin Tinubu domin samun abin da ake nema na ci gaba a kasar, Punch ta tattaro.

Tsohon gwamnan Kano ya ce Tinubu na bukatar hadin kai da kuma hakuri domin shawo kan matsalolin kasar..

Ganduje ya ce za a dakile matsalolin ƙasar

"Ina son rokon ƴan Najeriya da su kara hakuri musamman a bangaren rashin tsaro da kuma tattalin arziki."
"Ina da tabbacin cewa duka wadannan matsaloli an bayyana su a cikin wannan littafi da aka ƙaddamar."

- Abdullahi Ganduje

Akume yana tare da Ganduje kan Tinubu

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume a bangarensa shi ma ya roki ƴan kasar dasu ba Tinubu karin lokaci yayin mulkinsa.

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

Shugaban APC a Amurka, Farfesa Tai Balofin da abokin aikinsa, Farfesa Bolu Folayan ne suka rubuta littafin a kan jagorancin Tinubu.

Tinubu ya shirya korar wasu ministocinsa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai kori duka ministocinsa da ba su tabuka komai ba.

Shugaban kasar ya bayyana cewa zai ci gaba da kawo ababan more rayuwa ga al'ummar Najeriya baki daya.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da kungiyar Arewa Consultative Forum a birnin Abuja a jiya Alhamis 30 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.