Kananan Hukumomi: Tinubu Ya Bayyana Dalilin Kai Gwamnonin Jihohi 36 Kotu

Kananan Hukumomi: Tinubu Ya Bayyana Dalilin Kai Gwamnonin Jihohi 36 Kotu

  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta maka gwamnonin jihohi 36 a gaban kuliya manta sabo
  • Shugaban ya bayyana dalilin ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) a ranar Alhamis
  • A cewar shugaban, akwai bukatar gwamnoni su sakar wa kananan hukumomi mara, yana mai nuna damuwa kan yadda abin ya tabarbare

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin sa ke karar gwamnonin Najeriya 36 a gaban kuliya yayin da ya koka da yadda aka yi watsi da kananan hukumomi.

A ranar Alhamis, shugaban ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su ba da fifiko ga bukatun al’ummomin kananan hukumomi ta hanyar sakar masu mara a harkokin gudanarwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki zafi kan ministocinsa, ya fadi wadanda zai kora daga mukamansu

Bola Tinubu ya fadi dalilin kai karar gwamnonin jihohin kasar nan 36 a kotu
Tinubu ya nemi gwamnoni su amince da cin gashin kan kananan hukumomi. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

ACF ta zauna da Bola Tinubu

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwa kan taron, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajuri Ngelale ya ce Tinubu ya yi magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) a fadar gwamnati da ke Abuja.

Tinubu ya mika bukata ga manyan Arewa

Rahoton SaharaReporters ya nuna yadda Shugaba Tinubu ya koka kan yadda aka yi watsi da kananan hukumomi inda nan ne mafi yawan kuri'u ke fitowa.

Shugaban ya bukaci manyan Arewa da su tuntubi gwamnoni kan harkokin kananan hukumomin kasar nan domin ba da damar ba su 'yancin cin gashin kai.

Tinubu ya ce har sai shugabannin Arewa sun tashi tsaye tare da matsawa gwamnoninsu da tuntuba ne kananan hukumomi za su samu cin gashin kai.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, jam'iyyar Kwankwaso ta aike da saƙo ga Bola Tinubu

A halin yanzu dai gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Tinubu tana gaban kotu da gwamnonin jihohin Najeriya 36, ​​kan nema wa kananan hukumomi 'yanci.

Tinubu ya dauki zafi kan ministoci

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin sallamar duk wani ministansa da ba ya tabuka komai a mukamin da aka ba shi.

Tinubu ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Alhamis a lokacin da yake magana a wani taro da shugabannin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.